Karen Mota Ya Yi Karambani da Tirelar Dangote, Ya Ɓurma Gida Ya Murƙushe Yara
- Motar kamfanin Aliko Dangote ta kashe yara har uku a garin Zariya a wani mugun hadari
- Tirelar ta burma har uwar daka, ta raunta iyayen yaran wanda yanzu haka su ke jinya a asibiti
- Abin ya faru ne a garin Zariya da ke Jihar Kaduna, karen mota ne ya saci tirelar uban gidansa
Kaduna - Wata motar kamfanin Dangote ta yi sanadiyyar rasu rayuka a garin Zariya a jihar Kaduna, inda lamarin bai zo da dadi ba.
Abin da ya faru kuwa shi ne, Aminiya ta ce tirelar kamfanin ta shiga gida da kimanin karfe 3:00 na dare, ta bi ta kan yara su na barci.
Ana zargin motar dauko kayan ta kufcewa direban ne, shi kuma ya doshi gidan wani mutumi da aka ce sunansa Mal. Abdu Zailani.
Yara 3 sun mutu a gidan
A cikin dakin ne motar ta murkushe yaran Zailani, nan take su ka garzaya barzahu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Baya ga rasa yaran da aka yi, rahoton ya ce yanzu haka iyayen su na jinya a asibiti, sun samu raunuka a sakamakon wannan hadari.
Wannan gida ya na Unguwar Juma a birnin Zazzau a karamar hukumar ta Zariya.
Yadda mummunan abin ya faru
An bada sunan asalin direban motan da Malam Abdullahi, wani yaron aikinsa ne ya yi karambanin da ya salwantar da rayukan jama’a.
Shi babban direban bai san lokacin da karen motar ya dauki tirelar ba, har ya tafi yawo tare da abokansa bayan ya saci hanya a ranar.
Wani babban jami’in ‘yan sanda mai kula da shiyyar, DPO Kasim Abdul ya shaidawa jaridar cewa hadarin ya auku a tsakiyar makon nan.
Abdul ya ce sun yi nasarar zama da direban, ya sa hannu a takarda domin bincike.
Wani malamin addini a Unguwar Juma ya zanta da Legit.ng Hausa a jiya, ya kuma tabbatar da cewa abin ya faru ne yayin da ake barci.
Abin da ya faru a ranar
Ibrahim Zubairu wanda mazaunin unguwar ne ya ce bayan abin ya faru, mahaifin yaran ya fada masu su je su kwanta ganin akwai hadari a gari.
Farkwarsa ke da wuya, sai kurum ya tsinci kan shi a gadon asibiti. Sai bayan an sallamo shi ya fahimci cewa ‘ya ‘yansu uku sun rasu cikin daren.
Al-Mustapha, ‘dan autan Malam Abdu Zailani ne kadai wanda ya tsira domin yana tare da mahaifiyarsa.
Mahaifiyar yaran ta ce ta na iya tuna lokacin da ‘ya ‘yanta su ka tafi daki domin su kwanta, ita kuma ta rufe masu kofa sai ta wuce makwancinta a gidan.
Abin da ta ji bayan nan shi gini ya fado mata, sai ta ji Bayin Allah su na kokarin ceto su bayan motar ta auko masu, a haka aka iya kawo masu agaji.
Tun da abin ya faru, Malam Ibrahim Zubairu ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa ana zargin yaron motan ya tsere ya bar tirelar, ba a sake jin duriyarsa.
'Yan Najeriya na aiki da Dangote
Kwanaki wani rahoto ya zo da ya tabbatar da cewa sama da 'yan Najeriya 30,000 ne ke aiki a matatar man Dangote da ke garin Legas.
Kakakin kamfanin Dangote, Anthony Chiejine ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a matsayin martani kan wasu rade-radi da ake yi.
Asali: Legit.ng