Kungiyar NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Ranar 14 Ga Wata Idan FG Ba Ta Janye Karar Da Ta Shigar Ba
- Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan karar da ta shigar da kungiyar
- NLC ta ce idan gwamnatin ba ta janye karar ba za su shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Agusta
- Kungiyar ta bayyana wannan mataki ne yayin taron masu ruwa da tsaki na kungiyar a Abuja
FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Agusta idan har Gwamnatin Tarayya ba ta janye karar da ta shigar da kungiyar ba.
Kungiyar ta bayyana haka ne yayin ganawar masu ruwa da tsaki na kungiyar a yau Alhamis 3 ga watan Agusta a Abuja.
Ajaero ya yi barazanar durkusar da kasar kan dalilin kotu
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ya ce ma'aikatar shari'a da kotun masana'antu sun kaskantar da kansu ana amfani da su wurin lalata dimukradiyya, cewar Punch.
Juyin Mulki: Shehu Sani Ya Yi Hasashen Sakamakon Da Tawagar ECOWAS Karkashin Jagorancin Abdulsalami Za Ta Samo Nijar
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kungiyar ta ce duk da ta yanke shawarar janye zanga-zanga bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu za su ci gaba da yajin aiki a kan karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar, Daily Post ta tattaro.
Ta ce idan har gwamnatin ba ta janye karar da ta shigar ba, lallai za su shiga yajin aiki daga ranar 14 ga watan Agusta, cewar gidan talabijin na Channels.
NLC ta fitar da sanarwa a kan shiga yajin aiki
Yayin da ya ke bayyana matakin da masu ruwa da tsaki a kungiyar su ka cimma, Ajaero ya ce:
“Kwamitin ya yanke shawarar dakatar da zanga-zangar a kasa baki daya don tabbatar da gwamnatin ta cika alkawuran da ta dauka.
“Zamu tafi yajin aiki ‘yar gaba daya idan kotu ta tura wa shugabannin kungiya sammaci, mun kiraye su da su janye wannan karar kafin 11 ga watan Agusta.
“Za mu fara yajin aiki a kasa baki daya daga ranar Litinin 14 ga watan Agusta idan har wannan karar ba a janye ta ba.”
Kungiyoyin Kwadago Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Shirin Farawa
A wani labarin, Kungiyoyin Kwadago da suka fara zanga-zanga a fadin kasar sun ba da sanarwar janye yajin aikin da suke shrirn farawa a yau Alhamis.
Shugaban Kungiyar 'Yan Kasuwa, TUC, Festus Osifo shi ya bayyana haka a safiyar yau Alhamis 3 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng