Abdulsalam Ya Jagoranci Tawagar ECOWAS Zuwa Nijar Don Sulhu Bayan Juyin Mulki

Abdulsalam Ya Jagoranci Tawagar ECOWAS Zuwa Nijar Don Sulhu Bayan Juyin Mulki

  • Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Nijar don yin sulhu
  • Abdulsalami ya samu rakiyar Sarkin Musulmi, Sultan Abubakar Sa'ad da kuma shugaban hukumar ECOWAS, Alieu Touray
  • Tun bayan kaddamar da juyin mulki a Nijar, ake ta faman neman hanyoyin sulhu da za su kawo zaman lafiya a kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar ya jagoranci tawagar shugabannin ECOWAS zuwa Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar don yin sulhu.

Tawagar Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya ta isa birnin Yamai a jiya Laraba 2 ga watan Agusta.

Abdulsalam ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Niger don neman maslaha
Tsohon Shugaban Kasa, Abdulsalam Abubakar Ya Dira A Niger Tare Da Tawagar ECOWAS Don Tattaunawa Bayan Juyin Mulki. Hoto: LitCaf.
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne bayan kaddamar da juyin mulki da sojojin Nijar su ka yi a kan Mohamed Bazoum, Legit.ng ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Ya Ja Kunnen Gwamnatin Tinubu Kan Hambarar da Bazoum a Nijar

Abdulsalam ya samu rakiyar Sarkin Musulmi da sauran tawaga

Abdulsalami ya samu rakiyar Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar Sa'ad da kuma shugaban hukumar, Alieu Touray.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nijar a yanzu haka ta na karkashin jagorancin Abdourahmane Tiani wanda a baya shi ne shugaban masu tsaron tsohon shugaba Bazoum.

Janar Tiani a yayin juyin mulkin ya kama tare da tsare Mohamed Bazoum inda ya ke zargin shi da cin hanci da kuma rashin shugabanci mai inganci, cewar TheCable.

Kungiyar ECOWAS ta tura shugaban Jamhuriyar Benin, Patrice Talon da takwaransa na Chadi, Mahamat Deby don tattauna batun sakin Bazoum.

ECOWAS ta kakaba wa Nijar takunkumi

Kokarin yin hakan ya ci tura yayin da sojojin su ka ki amincewa da sakin Bazoum daga inda su ka boye shi, Tribune ta ruwaito.

Ganin haka, kungiyar ECOWAS ta yi ganawar gaggawa inda ta yi barazanar saka takunkumi ga kasar Nijar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: FG Da NLC Sun Fara Tattaunawa Kan Shirin Rage Radadi Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

Takunkumin sun hada da yanke alakar kasuwanci da ta kudade da kasar da kuma mamayar kasar da karfin soja idan ba su mayar da Bazoum mulki ba a cikin mako daya.

Sojojin A Nijar Sun Yi Fatali Da Bukatar ECOWAS Da Su Ba Da Mulki

A wani labarin, bayan Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta gargadi sojojin Nijar kan Mohamed Bazoum, sojojin sun yi fatali da bukatar kungiyar.

Kungiyar ta ce ta ba wa sojojin Nijar wa'adin kwana bakwai su saki Bazoum tare da mayar da shi madafun iko.

ECOWAS ta kuma ta yi barazanar saka takunkumin kasuwanci da yin amfani da karfin soja idan ba su mai da Bazoum kujerar shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.