An Kama Fasinja Kan Satar Naira Miliyan 1 a Cikin Jirgin Saman Abuja Zuwa Fatakwal
- An kama wani fasinja a jirgin saman Air Peace da ya tashi daga Abuja zuwa Fatakwal saboda satar naira miliyan 1
- An kuma samu fasinjan, wanda ba a bayyana sunansa ba da laifin satar kwamfuta a cikin jakar wani fasinjan jirgin
- An mika shi hannun 'yan sanda don gudanar da bincike, inda daga bisani kuma aka bayar da belinsa
Legas - Kamfanin jigila ta jiragen sama na Air Peace, ya ce an kama wani daga cikin fasinjojinsa a ranar Larabar makon da ta gabata, kan satar naira miliyan 1 daga jakar wani fasinja.
Mai magana da yawun kamfanin, Stanley Olisa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Legas.
Ya ce lamarin ya faru ne a cikin jirgi mai lamba P47192 da ya taso daga Abuja zuwa Fatakwal, a ranar 27 ga watan Yuli kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana samun yawaitar sace-sace a cikin jiragen sama
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya bayar da rahoton cewa, ana samun sace-sace a kamfanonin jiragen sama daban-daban da ke aiki a kasar nan a cikin 'yan kwanakin nan.
Olisa ya ce wanda ake zargin ya sace kudaden ne a cikin wata ambulan mai ruwan kasa, sai dai mai kudin ya yi nasarar kama shi da taimakon ma’aikatan kamfanin jirgin.
Ya kara da cewa, wanda ake zargin ya dauki jakar kwamfutar wani fasinja daga wurin da ake ajiye jakunkuna.
Bayan nan ne kuma wanda ya koma kujerar baya ya zauna kamar babu abinda ya faru.
Barawon ne ya fara kokarin ficewa bayan an sauka
Olisa ya bayyana cewa a lokacin da jirgin ya sauka, wanda ake zargin na gaba-gaba cikin masu yunkurin fita daga jirgin duk sanarwar da aka bayar ta cewa a bi a hankali.
Ya ce ana cikin hakan ne aka kama wanda ake zargin, inda aka same shi da kudaden kasashe daban-daban a tattare da shi.
Ya kara da cewa an mika wanda ake zargi hannun jami'an tsaron filin jirgin saman, inda daga bisani suka mika shi hannun 'yan sanda domin gudanar da bincike kamar yadda Premium Times ta wallafa.
Sai dai Olisa ya ce daga baya ya samu labarin cewa 'yan sandan sun sake shi ta hanyar bayar da belinsa.
Hadi Sirika ya yi magana kan halin da mutanen da suka yi hadarin jirgin sama suke ciki
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wani jirgi mai saukar angulu da ya yi hadari a birnin Legas.
Tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama a wani sako da ya wallafa ta kafar sada zumunta, ya bayyana cewa mutanen suna cikin yanayi mai kyau.
Asali: Legit.ng