Rundunar Yan Sandan Kano Za Ta Ba Da Kyautar Kudi Ga Wanda Ya Ke Da Bayani Kan Wasu 'Yan Daba 3
- Jami'an 'yan sanda a jihar Kano sun bayyana wasu 'yan daba uku da suka addabi mutane da ake nema ruwa a jallo
- Kwamishinan 'yan sanda, Muhammad Gumel shi ya bayyana haka yayin wasan sada zumunta tsakanin rundunar da tubabbun 'yan daba
- Ya ce duk wanda ya kawo ko wane daga cikinsu akwai kyautar N100,000 daga aljihunsa saboda sun ki amsa gayyata
Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta bazama neman wasu 'yan daba uku da suka addabi mutane ruwa a jallo.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Muhammad Gumel shi ya tabbatar da haka a ranar Laraba 2 ga watan Agusta.
Ya ce rundunar ta ware N100,000 ga duk wanda ya taimaka wurin ba da bayanin sirri don kama su a cikin mako daya, cewar Punch.
Abba Gida Gida Ya Ce Ya Na Bukatar Biliyan 6 Don Wadatar Da Makarantun Kano Da Kujerun Zama, Ya Koka Da Mulkin Ganduje
Ya bayyana yadda tubabbun 'yan daban su ka halarci wasan kwallon kafa
Gumel ya bayyana haka ne yayin wasan sada zumunta tsakanin hukumar da kuma tubabbun 'yan daba a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano, Newstral ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce sun ayyana neman 'yan daban ruwa a jallo saboda sun ki amsa gayyata tare da mika kansu ga hukumar don yin sulhu.
Ya kara da cewa tubabbun 'yan daba 99 ne suka halarci wasan yayin da ta gayyaci 30 kacal daga cikinsu, Vanguard ta tattaro.
Ya bayyana sunayen 'yan daban da ake nema da Barakata da ke Dorayi da Hantar Daba sai kuma Chile mai Doki da ke Tudun Fulani.
Gumel ya ce zai ba da kyauta ga duk wanda ya taimaka da bayanai
Ya ce:
"Mu na kokarin dakile laifuka a Kano ta fannin sulhu da kuma hanyoyin zaman lafiya daban-daban.
"Mun gayyaci 30 ne kadai daga cikin 'yan daban amma abin mamaki 99 sun halarta tare da tuba da kuma ajiye makamansu.
"Akwai guda uku da suka ki halarta su ne Hantar Daba da Chile mai Doki sai kuma Barakata, duk wanda ya kawo daya daga cikinsu ya na da kyautar N100,000.
"Idan kuma al'umma su ka kawo su duka uku akwai kyautar N300,000 daga aljihu na."
'Yan Sanda Sun Bazama Neman Makera Masu Kera Wukake Da Ake Ta'addanci Da Su A Kano
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta shiga gari neman wasu makera da ake zargi da taimakon ta'addanci.
Ana zargin makeran da kerawa 'yan ta'adda wukake da sauran makamai da suke amfani da su wurin aikata laifuka.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Muhammad Gumel shi ya bayyana haka yayin ganawa da 'yan jaridu.
Asali: Legit.ng