Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

  • Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC sun yi zama da Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock Villa
  • Kwamred Joe Ajaero ya ce an yi masu alkwarin gyara matatar man fetur nan da Disamban bana
  • Shugaba Tinubu ya yi haramar yi wa ma’aikata karin albashi a sakamakon tashin farashin fetur

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Shugabannin kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC, sun yi bayanin makomar zaman da su ka yi da Mai girma Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero ya shaida cewa Bola Ahmed Tinubu ya daukan masu wasu alkawura.

Kwamred Joe Ajaero ya ce shugaban Najeriyan ya tabbatarwa al’ummar kasar nan cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an gyara matatar mai a bana.

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago
Shugaban kasa Bola Tinubu da 'Yan kwadago Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Za a maida hankali a kan gas

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Shugaban na NLC yake fadawa manema labarai zuwa Disamba za a samu matatar da ke tace danyen mai, ana sa ran hakan zai rage tsadar litar fetur.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto Ajaero yana bayanin yadda shugaban kasar ya sha alwashin shiga yarjejeniya da NLC domin a yi gaggawar kara albashin ma’aikata.

Har ila yau, ‘yan kwadago sun ce Tinubu ya dauki alkawarin cewa a mako mai zuwa za a fito da tsarin yadda Najeriya za ta koma amfani da CNG.

Bayan an gama zanga-zanga a fadin jihohi 36 da birnin Abuja, Kwamred Ajaero ya ce za su dawo kan tebur domin cigaba da tattaunwa da gwamnati.

Jawabin Kwamred Ajaero

“Ya kamata mu sanar da ‘Yan Najeriya cewa nasarar da aka samu a sakamakon zanga-zangar shi ne bukatar shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: FG Da NLC Sun Fara Tattaunawa Kan Shirin Rage Radadi Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

"Sanata Ahmed Bola Tinubu ya nemi ya kebe bayan labule da shugabannin NLC da TUC.
"Taron ya haifar da ‘da mai ido sosai domin an cin ma nasarori a game da abubuwan da su ka shafi aikin kwamitin shugaban kasa kan tallafin fetur."

Kwamred Joe Ajaero

Zuwa yanzu, ‘yan kwadagon sun ce za su ba gwamnatin tarayya lokaci domin Mai girma shugaban kasa ya iya cika alkawuran da ya daukan masu.

Za a samu Ministoci rututu a Najeriya

Ku na da labari Shugaban kasa yana neman nada Ministoci 47 adadin da ya zarce tarihin da Muhammadu Buhari ya bari a lokacin da ya bar mulki.

Tsofaffin Gwamnonin jihohi 10 aka zaba a Ministocin da za su yi aiki da Bola Tinubu, sannan mata tara za su zauna a Majalisar FEC, mafi yawa tun 1999.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng