Abba Gida Gida Na Kano Na Bukatar Fiye Da Biliyan 6 Don Samar Da Kujerun Zama A Makarantun Jihar

Abba Gida Gida Na Kano Na Bukatar Fiye Da Biliyan 6 Don Samar Da Kujerun Zama A Makarantun Jihar

  • Gwamnatin jihar Kano na bukatar fiye da Naira biliyan shida don samar da kujerun zama ga daliban firamare da sakandare
  • Kwamishinan ilmi a jihar, Haruna Umar Doguwa shi ya bayyana haka a Kano yayin karbar bakwancin jami'an hukumar UNICEF
  • Doguwa ya koka kan yadda harkar ilimi ya shiga mawuyacin hali a hannun gwamnatin da ta shude

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta ce su na bukatar Naira biliyan shida don samar da kujeru a makarantu.

Akalla makarantun firamare da sakandare fiye da 9,000 ne ke bukatar kujerun zama don inganta karatunsu.

Abba Kabir na bukatar Naira biliyan 6 don samar da kujerun zama a makarantu
Gwamna Abba Kabir Na Jihar Kano Ya Fadi Adadin Kudaden Da Ya Ke Bukata Don Samar Da Kujerun Makaranta. Hoto: SolaceBase.
Asali: UGC

Kwamishinan ilimi a jihar, Haruna Umar Doguwa shi ya bayyana haka a yau Laraba 2 ga watan Agusta yayin ganawa da jami'an hukumar UNICEF.

Abba Kabir ya umarci ma'aikatar ilimi ta yi lissafin abin da ake bukata

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Gonan Sanata a Arewa, An Rasa Rai

Ya ce hakan na zuwa ne bayan halin ha'ula'i da fannin ilimi ya shiga a hannun gwamnatin baya, Aminiya ta tattaro.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Umar ya ce dalilin haka, Gwamna Abba Kabir ya umarci ma'aikatar ilimi ta ba da kididdigar abubuwan da ake nema a makarantun.

Doguwa ya ce:

"A kididdigar da muka yi mun gano cewa dalibai fiye da miliyan biyar ba su da kujerun zama da tebura.
"A wata ziyara da na kai da kai na, na ga yara fiye da 5,000 a zaune a kasa a makarantar Dawanau Special Primary school da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.
"Kun ga yadda lamarin ilimi ya dawo a jihar ko, abin ya yi muni."

Ya bayyana matsalolin da makarantun ke fuskanta

Doguwa ya kara da cewa sauran matsalolin da makarantun ke fuskanta akwai rashin kayan aiki na malamai da kuma ababan more rayuwa a makarantun.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Raba Buhuna 36, 000 na Kayan Abinci Kyauta a Kowane Gari

Ya ce wata babbar matsala ita ce yaran da ba sa zuwa makaranta wanda hakan ya ruguza harkar ilimi a jihar gaba daya, cewar The Sun.

Gwamnatin Kano Ta Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO Don Inganta Ilimi

A wani labarin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya biya wa dalibai 55,000 kudaden jarabawar NECO a jihar.

Abba ya ce ya yi hakan ne don inganta harkar ilimi a jihar da ke faman tabarbarewa.

Ya shawarci daliban da su yi karatu tukuru don ganin sun ci jarrabawa ba tare da ba wa iyayensu kunya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.