Hadi Sirika Ya Ce Mutanen Cikin Jirgin Saman Da Ya Yi Hadari a Legas Na Cikin Kyakkyawan Yanayi

Hadi Sirika Ya Ce Mutanen Cikin Jirgin Saman Da Ya Yi Hadari a Legas Na Cikin Kyakkyawan Yanayi

  • Wani ɗan ƙaramin jirgi mai saukar angulu da ya yi haɗari a Legas ya tayar da hankulan mazauna yankin
  • An yi nasarar ceto mutanen da ke ciki da rayukansu duk da kamawa da wutar da jirgin ya yi jim kaɗan bayan faɗuwarsa
  • Hukumomi sun ce haɗarin ya rutsa da 'yan Najeriya da wasu 'yan ƙasashen waje, waɗanda yanzu haka ke karɓar kulawa a asibiti

Jihar Legas - Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, ya ce mutanen jirgi mai saukar angulu mai lamba 5N CCQ da yayi haɗari a Oba Akran da ke jihar Legas na nan cikin yanayi mai kyau.

Sirika ya bayyana hakan ne a shafinsa na ranar Twitter ranar Talata, 1 ga watan Agusta.

Hadi Sirika ya yi magana kan hadarin jirgin saman da ya faru a Legas
Hadi Sirika ya ce da jirgi ya fadi da su a Legas na cikin yanayi mai kyau. Hoto: Channels TV, Twitter/@hadisirika
Asali: UGC

Sirika ya miƙa godiyarta ga Ubangiji

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya 'Yan Bindiga Suka Kwamushe Ni, Babban Boka Ya Yi Bayani Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci

Hadi Sirika ya miƙa godiyarsa ga Ubangiji, da ya tseratar da rayuwar mutanen da ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma roƙi Ubangiji da ya ci gaba da kare rayukan 'yan Najeriya daga haɗarurruka, sannan kuma ya yi fatan cewa binciken da ake yi zai taimaka wajen kare faruwar hakan a gaba.

Ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar mutane su bayar da haɗin kai wajen tsare inda lamarin ya faru domin gudanar da sahihin bincike.

An shiga ruɗani, yayin da jirgin sama ya faɗi a Ikeja da ke Legas

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan haɗarin ƙaramin jirgin sama mai saukar angulu da aka samu a yankin Oba Akran da ke birnin Legas.

Da faɗowar jirgin ne ya kama ci da wuta, wanda hakan ya sanya fargaba a cikin mutanen da ke yankin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Stella Okotete: Lauya Ya Bukaci Majalisa Ta Fatattaki Daya Cikin Ministocin Tinubu, Ya Bada Kwakkwaran Dalili

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce ba za a iya gane ko wane kalar jirgi ba ne, inda ya kuma bayyana cewa bai san halin da mutanen ciki suke ba.

Jirgin sama ya yi saukar gaggawa a Abuja

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan jirgin sama maƙare da fasinja da ya yi saukar gaggawa a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Hakan ya faru ne sanadiyyar matsalar da ya samu jim kaɗan da tashinsa daga Abuja da zummar zuwa garin Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng