Karin Albashi Na Nan Tafe, Tinubu Ya Bai Wa Ma'aikata Tabbaci

Karin Albashi Na Nan Tafe, Tinubu Ya Bai Wa Ma'aikata Tabbaci

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ana duba batun kara wa ma'aikatan Najeriya sabon albashi mafi karanci
  • Yayin da ya ke jawabinsa ga yan kasa a ranar Litinin, shugaban kasar ya ce akwai yarjejeniya tsakanin kungiyoyin kwadago da gwamnati, kuma za a yi tanadi a kasafin kudin kasa
  • Shugaban kasar ya yi jawabi ga yan kasar gabanin shirin yajin aiki da NLC da TUC ke shirin yi saboda cire tallafin mai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago na aiki don ganin an fitar da sabon albashi mafi karanci.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabi na kai tsaye da ya yi a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, wanda Legit.ng Hausa ta yi nazari a Channels Television.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Yi Babban Naɗin Na Hannun Dama, Ya Naɗa Tsohon Hadimin Osinbajo

Shugaba Tinubu ya yi wa ma'aikatan Najeriya albishir da karin albashi
Tinubu ya ba wa ma'aikatan Najeriya tabbacin karin albashi na nan tafe. Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu, yayin jawabin ga yan Najeriya kan zafin cire tallafin man fetur, ya ce ana shirin bullo da sabon albashi mafi karanci, ya kara da cewa kwamitin bai wa shugaban kasa shawara za ta tsayar da tallafin da ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamitin bai wa shugaban kasa shawara kan tallafin rage radadi ya kunshi wakilai daga gwamnatin tarayya, ciki har da Kungiyar Kwadago, NLC, da Kungiyar Masu Sana'o'i, TUC.

Yayin jawabin, shugaban kasar ya bayyana cewa da zarar tawagar da cimma matsaya kan albashin mafi karanci, gwamnatinsa za ta yi tanadin biya a kasafin kasa.

Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kawowa yan kasa sauki biyo bayan cire tallafin man fetur

Sanarwar da Tinubu ya yi na cewa 'tallafin mai ya zo karshe' a ranar 29 ga watan Mayu ya janyo tashin farashin kayayaki a kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ji Ta Mutane, Kaura Zuwa Fadar Shugaban Kasa Bayan Shafe Watanni 2 A Asokoro, Ya Bayyana Dalili

A jawabinsa, shugaban kasar ya jinjinawa kamfanoni masu zaman kansu bisa kara wa ma'aikatansu albashi.

Ya ce:

"A kan batun, muna aiki tare da kungiyar kwadago don bullo da sabon albashi mafi karanci ga ma'aikata. Ina son fada wa ma'aikatanmu wannan: karin albashinku na tafe."

Atiku ya soki Tinubu, ya ce 'jawabin Tinubu bata lokaci ne'

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Atiku Abubakar, tsohon matamakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, ya bayyana jawabin Shugaba Tinubu na ranar Litinin a matsayin yaudara.

Shugaban na PDP, cikin sanarwar da ya fitar bayan jawabin shugaban kasar, ya bayyana matakin a matsayin bata lokaci.

Ya ce jawabin na Tinubu borin kunya ne kawai bayan gwamnatinsa ta cire tallafin mai ba tare da yin tanadi mai kyau don saukaka wa yan Najeriya wahalhalu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164