'Yan Sanda Sun Cafke Mutane Fiye Da 100 Kan Zargin Satar Kayan Gwamnati A Adamawa

'Yan Sanda Sun Cafke Mutane Fiye Da 100 Kan Zargin Satar Kayan Gwamnati A Adamawa

  • Rundunar ‘yan sandan Adamawa sun cafke mutane fiye da 100 da ake zargi da hannu cikin sace-sacen kayan gwamnati
  • Kakakin rundunar a jihar, Suleiman Nguroje shi ya bayyana haka a yau Litinin 31 ga watan Yuli a Yola babban birnin jihar
  • Ya ce tun farko jami’ansu sun cafke mutane 25 yayin da daga baya sauran jami’an tsaro suka kama akalla mutane kusan 100

Jihar Adamawa – Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta tabbatar da kama mutane fiye da 100 da ake zargin da fasa rumbun gwamnati tare da satar kayan abinci da sauran abubuwa.

Kakakin rundunar a jihar, Suleiman Nguroje shi ya bayyana haka a yau Litinin 31 ga watan Yuli a Yola.

'Yan sanda sun kama wadanda ake zargi 100 kan zargin fasa rumbun gwamnati
Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Mutane Fiye Da 100 Kan Zargin Fasa Siton Gwamnati A Adamawa. Hoto: Punch.
Asali: UGC

Nguroje ya bayyana wa TheCable cewa a farko jami’ansu sun kwamushe mutane fiye da 25, yayin da sauran jami’an tsaro suka kama wasu da jimillar ta kai kusan mutane 120.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hanyoyi 4 na kare kai daga fadawa ta'addanci bayan cire tallafin man fetur

'Yan sanda sun kama batagarin da suka fasa rumbun gwamnati

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A farko, mun kama mutane 25, daga baya kuma an kama wadansu da aka samu da kayan sata wanda hakan ya sa suka zama abin zargi.
“A yanzu haka, muna da kusan mutane 120 da muke zarginsu da aka kama, muna shirye-shiryen kai su kotu, zan ba da sanarwa daga baya akan wannan lamari kuma zan sanar da ku.”

Idan ba a mantaba, a jiya Lahadi 30 ga watan Yuli an samu hatsaniya yayin da mutane suka fasa rumbun gwamnatin jihar da kuma na wasu masu zaman kansu tare da satar kayayyaki a ciki, Premium Times ta tattaro.

Daga cikin kayan da aka sata akwai masara da shinkafa da wake da dawa da zannuwa da katifu da bokatai na roba da sauransu.

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: Yan Sanda Sun Yi Ram Da Matasa 6 Kan Fashi Da Makami a Bauchi

Shaidun gani da ido sun tabbatar cewa hakan bai rasa nasaba da yadda mutane ke shan wahala tun bayan cire tallafin mai da aka yi a kasar da ya jawo tashin farashin kaya.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da tsaron kadarorin gwamnatin jihar

Gwamnatin jihar daga bisani ta saka dokar ta baci har na tsawon sa’o’i 24 don dakile ci gaba da sace-sacen, cewar Leadership.

Nguroje ya ce an tura jami’an tsaro don kare kasuwanni da kuma kadarorin gwamnati da na masu zaman kansu da kuma tabbatar da an bi dokar kamar yadda ya dace.

A karshe ya yi alkawarin kwato kayayyakin da aka sacen da kuma tabbatar da wandanda ake zargi sun fuskanci shari’a.

Hukumar NEMA Ta Kara Tsaro A Rumbun Abinci Na Kaduna Bayan Abin Da Ya Faru A Adamawa

A wani labarin, Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa, NEMA a jihar Kaduna ta kirayi gwamnatin jihar Kaduna ta tsaurara matakan tsaro a rumbunan abincinta.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Matasan da Ba Ruwansu Sun Mutu Yayin da Jami'ai Suka Kai Farmaki a Jihar APC

Kodinetan hukumar a jihar, Abbani Imam shi ya bayyana haka inda ya kwatanta hakan da abin da ya faru a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.