An Samu Asarar Rai Yayin Gwamnatin Jihar Imo Ta Lalata Matsugunan Hausawa
- Ƴan kasuwar Hausawa da su ke neman na abinci a jihar Imo sun tafka gagarumar asara bayan jami'an gwamnati sun farmake su
- Jami'an gwamnatin dai sun ƙona shaguna da gidajen Hausawa a wasu kasuwanninsu guda uku a jihar
- Ƴan kasuwar dai sun tafka asara mai yawa yayin da har wani daga ciki aka halaka da runata wani daban
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Imo - An halaka mutum ɗaya tare da raunata wani daban yayin da aka ƙona shaguna da gidaje masu yawa lokacin da jami'an gwamnatin jihar Imo suka dira a matsugunan Hausawa a ƙaramar hukumar Owerri ta Yamma a jihar Imo.
Majiyoyi da dama sun gayawa jaridar Daily Trust cewa, jami'an gwamnatin na hukumomin raya birnin Owerri (OCDA) da kula da muhalli (ENTRCO), tare da wasu ƴan sanda sun ƙona shaguna da kayayyaki a Kwanar Avu da Kasuwar Hausawa, Nekede No 1 da kasuwar Arugu.
An ƙona kasuwannin ne a ƙoƙarin gwamnatin jihar na cire dukkanin wasu haramtattun tantuna da gine-gine a kasuwannin.
Wani mai suna Nura Umar, shugaban matasa a kasuwar Nekede No 1, ya bayyana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Gidaje da shaguna da dama mallakin ƴan Arewa aka ƙona, da yawa daga cikinmu a cikin daji mu ka samu mafaka sannan har masallacin Juma'ar mu jami'an hukumomin tare da ƴan sanda suka ƙona."
Umar ya bayyana cewa tashin hankalin ya fara ne ranar Alhamis inda ya ruru sosai ranar Lahadi lokacin da jami'an ƴan sanda bisa gayyatar jami'an hukumar ENTRACO, suka harbi wani ɗan kasuwa mai suna Mudashir Muhammad mai shekara 35 tare da raunata wani daban.
Gwamnatin jihar na son tsaftace birnin Owerri
A shekarar da ta gabata gwamnatin jihar Imo ta hannun hukumar OCDA ta sanar da shirin tsaftace birnin daga kasuwancin bakin tituna da aje ababen hawa ba bisa ƙa'ida ba.
Shugaban hukumar OCDA, Francis Chukwu, a wancan lokacin ya gana da shugabannin Hausawa a jihar domin neman haɗin kansu wajen gudanar da aikin.
Ƴan sanda sun musanta ƙona shagunan Hausawa
Sai dai, babu tabbacin ko abinda ya faru a kasuwannin guda uku na daga cikin shirin da gwamnatin jihar take da shi, domin kwamishinan watsa labarai na jihar, Declan Emelumba, bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba.
Sai dai kwamishinan ƴan sandan jihar Imo, Mohammed Barde, a wata tattaunawa da manema labarai ranar Lahadi, ya musanta zargin cewa an ƙona kasuwannin guda uku, inda ya ce gobara ce ta kama a kasuwar Avu.
Ƴan kasuwan da lamarin ya ritsa da su dai sun bayyana babu ƙamshin gaskiya a maganar kwamishinan ƴan sandan, inda suka ce babu wata gobara da ta auku a kasuwannin, kawai dai jami'an gwamnatin ne da ƴan sanda suka aikata musu hakan.
Wani mai suna Musa Isa wanda yake da shagun siyar da kayan masarufi, ya bayyana cewa ya tafka asara sama da ta N10m.
An Halaka Basarake a Jihar Imo
A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun halaka wani basarake a jihar Imo bayan sun kai masa hari har cikin fadarsa.
Ƴan bindingan dai sun halaka basaraken na Nguru dake a ƙaramar hukumar Aboh Mbaise bayan sun kutsa kai cikin fadarsa.
Asali: Legit.ng