Kwamiti Ya Karbo Motoci 48 Daga Hannun Tsohon Gwamnan PDP da Mukarrabansa
- Gwamnatin Hyacinth Alia ta na cigaba da karbe dukiyoyin al’umma da ta ce an dauke a mulkin PDP
- Hinga Biem ya shaida cewa akwai motoci kusan 50 da yanzu sun dawo karkashin gwamnatin jihar Benuwai
- Shugaban kwamitin ya ce mukarraban tsohuwar gwamnatin za su yi bayanin cire lambobin injin motoci
Benue - Kwamitin Hinga Biem wanda aka ba alhakinkarbo dukiyar gwamnati da aka yi gaba da ita a jihar Benuwai, tana cigaba da gudanar da ayyukanta.
A ranar Lahadi, The Nation ta rahoto Hinga Biem ya na mai bayanin sun karbe motoci 48 a hannun tsohon Gwamna Samuel Ortom da manyan jami’ai.
A cewar Biem, wadannan motoci su na cikin dukiyoyi da kadarorin gwamnatin Benuwai da aka saidawa manyan mukarraban jihar ko su ka dauke su.
Ortom ya ga ta kan shi
Ana zargin hakan ya faru a lokacin da Mai girma Samuel Ortom yake kan kujerar Gwamna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban kwamitin ya ce a cikin kayan gwamnati da su ka karbo har da taraktoci, motocin jami’an tsaro da motocin da ake amfani da su na bacin-rana.
An samu mutane biyar da su ka dawo da motocin da ke hannunsu da kansu, zuwa yanzu kwamitin ya aika takarda ga mutum 36 da sun rike mukamai.
"Bari mu ce, alal misali, Gwamnan Benuwai yana da motoci a jerin tawagarsa. Babu laifi ya tafi da motocinsa da na mukarrabansa.
Amma akwai abin tambaya kan daukar motocin ‘yan jarida, motar dogarai, motocin jami’an tsaro da na asibiti wanda na jama’a ne."
-Hinga Biem
Rahoton akwai wasu motocin da aka cire masu lambar inji, kwamitin ya ce sai an yi wa jami’an tsaro bayani dalla-dalla a kan abin da ya sa aka yi hakan.
Ana ikirarin da aka shiga shagon Ortom, an yi gaba da motocin wasu da aka kawo gyara, Biem ya ce idan ta tabbata, to za su maidawa mutane dukiyarsu.
Biem: "Ba a dauki motocin mutane ba"
Ku na da labari jam’iyyar PDP ta na ikirarin da aka shiga garejin tsohon gwamnan Benuwai, an dauki motocin wasu Bayin Allah da su ka kawo gyara.
Kwamitin Biem ya ce idan akwai takardu dauke da hujjoji, za a maidawa mutane motocinsu, zuwa yanzu ba a samu wanda ya gaskata hakan ba.
A ranar 16 ga watan Yuni, Gwamna Hyacinth Alia ya kafa wannan kwamiti da nufin dukiyoyin al’umma da ake tsoron sun fada hannun wasu tsiraru.
Asali: Legit.ng