Sanata Orji Kalu Ya Roki NLC Ta Fasa Shiga Yajin Aiki, Ya Ce Talaka da Mai Kudi Kowa Na Tare Duka a Najeriya

Sanata Orji Kalu Ya Roki NLC Ta Fasa Shiga Yajin Aiki, Ya Ce Talaka da Mai Kudi Kowa Na Tare Duka a Najeriya

  • Daya daga cikin masu fada a ji a Najeriya ya bayyana cewa, ‘yan kasar na cikin wani yanayi mai ban tsoron gaske
  • Orji Uzor Kalu ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri da halin da ake ciki a yanzu, ya fadi dalilansa na haka
  • A cewarsa, yajin aikin da NLC za ta shiga zai iya jawo rikici da tashin hankali a fannin tattalin arzikin kasar nan

Najeriya - A wani bidiyon da sanata Orji Uzor Kalu ya fitar, ya bayyana rokonsa ga kungiyar kwadago kan shirin yajin aiki da take yi nan kusa.

Ya bayyana cewa, akwai bukatar kungiyar ta NLC ta yi duba da irin wahalar da ‘yan kasar ke ciki tare da daga kafa da shirin yajin aikin.

Hakazalika, ya yi tsokaci da cewa, shi kansa mai kamfani ne da ke da mutanen da ke aiki a karkashinsa, don haka ya san zafin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Kalu ya roki NLC kan yajin aiki
Ku fasa yajin aiki, Kalu ga NLC | Hoto: @OUKtweets
Asali: Facebook

Yajin NLC zai rusa tattalin arziki

A cewar Kalu, yajin aikin da NLC din ke shirin yi zai iya durkusar da tattalin arzikin Najeriya, wanda a yanzu ma tuni ya riga ya shiga halin ni ‘ya su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“Ina kira ga kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da kada ta yi wa tattalin arzikin kasa illa a shirin yajin aikin da take yi.”

Ni da shugaban kasa mun san halin da ake ciki

Da yake karin haske game da halin da mutane ke ciki a kasar, ya bayyana cewa, babu mai kudi ko talaka, kowa na shan wahala a Najeriya.

A kalamansa:

“Lokaci ne da dukkan ‘yan Najeriya ke shan wahala, masu hannu da shuni da talakawa. Ni mutum ne mai ma’aikata a karkashi na kuma na san cewa abubuwa sun yi kunci. Ko shugaban kasa ya san haka.”

Kara karanta wannan

Albashin Aikin Gwamnati Zai Koma ‘Iyaka Kokarinka a Ofis Iyakar Kudinka’ a Wata

Sabuwar matsala ta bullo, NLC ta ce za ta shiga yajin aiki

A tun farko, kungiyar kwadugo ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 7 ta sake nazari kan tsare-tsarenta da suka haddasa tsadar rayuwa a Najeriya.

Vanguard ta rahoto cewa NLC ta buƙaci FG ta janye wadannan tsare-tsare da suka jefa talakawa cikin halin kakani-kayi, ciki harda tashin farashin litar man fetur na kwanan nan.

Kungiyar ta bai wa gwamnati mako daya ta sauya wadannan tsare-tsaren na yaki da talakawa ko kuma a fuskanci yajin aikin gama gari daga ranar 2 ga watan Agusta, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.