Tinubu: Yadda Za a Ɓarka Ma’aikatu Domin Ministoci Su Samu Muƙaman Da Za Su Riƙe

Tinubu: Yadda Za a Ɓarka Ma’aikatu Domin Ministoci Su Samu Muƙaman Da Za Su Riƙe

  • Za a ga sauye-sauye a Ma’aikatun gwamnatin tarayya zuwa lokacin da za a rantsar da Ministoci
  • Sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai zo da irin na sa tsare-tsaren na dabam a Najeriya
  • Akwai ma’aikatun da za a soke, za a barka wasu, yayin da Tinubu zai kirkiro wasu sababbin ma’aikatu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Alamu sun nuna gwamnatin tarayya za tayi wa ma’aikatun Najeriya garambawul, hakan ya biyo bayan fitar da sunayen Ministoci.

Rahoton Punch ya nuna gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za tayi wa ma’aikatu kwaskwarima ta hanyar sokewa, hadawa da kirkirar sababbi.

Sabon shugaban Najeriyan zai kuma aiwatar da wasu shawarwarin kwamitin Stephen Oronsaye.

Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Ma'aikatun da abin zai shafa

Binciken ya nuna sauyin zai shafi ma’aikatun ilmi, matasa da wasanni, noma da rayar karkara, ma’adanai, gidaje da ayyuka da na lantarki.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaba Tinubu Ya Fada Mana a Aso Villa Inji Shugabannin ‘Yan Kwadago

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Za a samu ma’aikatu biyu a karkashin ma’aikatar, wata za ta kula da matakin farko na ilmi sai dayar ta rika kula da ilmin gaba da sakandare.

A ma’aikatar gidaje da ayyuka, za a samu ma’aikata ta musamman da za ta kula da titunan tarayya sai ma’aikatar da za ta ji da dawainiyar gidaje.

Ma’aikatar jin-kai, bada agajin gaggawa da cigaban walwala za ta maida hankali wajen cigaban al’umma, a maida hankali ga walwalan jama'a.

Ma'aikatar tattalin arziki

Idan aka zo ma’aikatar tattalin arziki, za a fitar da bangaren kudi da na kasafi, sai a barka ma’aikatar tsare-tsare, watakila ta samu Minista kan ta.

Kwaskwarimar da za ayi za ta shafi ma’aikatar kasuwanci da hannun jari da nufin bunkasa tattali.

Mu na tunanin za a samu ma’aikatar makamashi daga ta wuta, za a kuma yi canji a ma’aikatar harkokin mai, za a maida hankali kan harkar gas.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 20 da Hadimai 18, Ya Raba Ma'aikatar Ilimi Gida Biyu

A ma’aikatar noma, za a iya samun Minista mai lura da sha’anin aikin gona da wani takwaransa da zai rike ma’aikata dabam domin raya karkara.

El-Rufai a gwamnatin Tinubu

Shekara daya kafin nada Ministoci, an ji labarin yadda Bola Ahmed Tinubu ya nemi alfarmar Malam Nasir El-Rufai, ya yi aiki da gwamnatinsa.

A lokacin ‘Dan takaran na APC ya lallabi Gwamnan Kaduna, ya zauna a maimakon ya tsere daga Najeriya, kamar yadda ya yi a mulkin 'Yaradua.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng