“Na Cire N35k:” Ma’aikacin Banki Ya Bayyana Yadda Ya Yi Amfani Da Katin ATM Din Kwastoma Ba Tare Da PIN Ba
- Wani tsohon ma'aikacin banki ya bayyana yadda ya zire kudi da katin ATM din wata kwastoma ba tare da PIN dinta ba
- Uchenna Emmanuel ya ce an yi kutse a na'urar PoS da ya yi amfani da ita, wanda hakan ne ya ba shi damarar aikata ta'asar
- Ya ce sau biyar kawai ya cire jimillar N35,000 daga asusun bankin kwastomar
Wani tsohon ma'aikacin banki, Uchenna Emmanuel, ya bayyana yadda ya yi kuskuren amfani da katin ATM din kwastoma wajen cire kudi sau biyar.
Tsohon ma'aikacin bankin na daya daga cikin bankunan zamani ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, 2023, yayin da rundunar yan sandan Ondo ta gurfanar da shi a Akure.
An yi kutse a na'urar Pos din
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Emmanuel ya yi ikirarin cire kudin daga asusun bankin sau biyar domin siyan kayayyaki da ya kai N35,0000.
“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, an yi kutse na'urar Pos dinsa, wanda hakan ke sa ayi damfara da ita cikin sauki ba tare da lambobin sirri wato PIN ba.
Jaridar Punch ta nakalto yana cewa:
"Na yi amfani da katin kwastoman bisa kuskure wajen siyan abubuwa daga wani kamfani. Na zata katina ne.
"Daga baya sai manajan ya tsinci katin a hannuna, sannan ya sallame ni nan take.
"Sun tambayeni ta yadda na san PIN din kwastoman, sai na ce na yi amfani da PIN dina ne. Sun kawo wani Pos din, sannan wani dan sanda ma ya yi kokarin gwada kain ATM dinsa, abun ya yi cikin nasara.
"Na yi amfani da katin kwastoman sau biyar."
'Yan Damfara Sun Yi Kutse a Bankunan Najeriya, Sun Sace N1bn Daga Asusun Kwastomomi
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa kusan Naira Biliyan 1 ne aka yi hasararsu ta dalilin zamba da sata ta hanyoyin biyan kudi da mu'amalar yau da kullum a cikin kwata na farko na 2023.
Hakan ya biyo bayan fargabar da Hukumar Inshorar Ajiyar Kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana kan yawaitar satar da ake samu a bankuna.
An bayyana hakan ne a cikin wani rahoto mai suna, "Rahotanni kan zamba da sata a bankunan Najeriya", wanda cibiyar horar da harkokin kudi (FITC) ta buga kwanan nan.
Asali: Legit.ng