Masu PhD 3: Matakin Karatun Mutanen da Tinubu Ya Zaba a Matsayin Ministocinsa
A ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya mika jerin sunayen ministocinsa 28 ga majalisar dokokin kasar domin tantance su, kafin cikar wa’adin kwanaki 60 da dokar kasar ta kayyade.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rahotanni sun shaida cewa, an zabo wadanda aka nadan ne daga jihohi 25 na tarayyar kasar - ban da jihohi 11.
Wani binciken da TheCable Index ta yi ya nuna cewa mafi karancin matakin karatun wadanda aka zaba shine digiri na farko kuma mafi girma shi ne mai digirin digirgir.
Yayin da mutane 16 da Tinubu ya zaba ke da digiri biyu, tara daga cikin 28 din na da digirin farko, inda mutum uku kuwa ke da digirin digirgir.
Biyu daga cikin wadanda ke da digirin digirgir din ma sun yi aiki da samun gogewar da suka za su iya zama farfesoshi.
Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su waye ya kamata a nada kujerun minista?
A cewar sashe na 147(5) na kundin tsarin mulkin kasar, mutum ba zai cancanci kujerar minista ba har “sai dai idan ya cancanta a zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai”.
Sashi na 65 (1) (a) na kundin tsarin mulkin kasar ya bayyana cewa mutum zai iya takarar majalisar wakilai ne idan ya samu ilimi har zuwa akalla matakin karantun satifiket ko makamancinsa.
Duk da cewa dukkan wadanda aka nada sun cancanta a bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar, a baya ‘yan majalisar sun bayyana ra’ayinsu game da mafi karancin matakin karatu.
A watan Janairun 2022, Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya ce akwai bukatar a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin kara tsaurara cancantar matakin karatu a zaben ofishin majalisar dokokin kasar.
Hankula Sun Tashi Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai A Shagon Aski, 'Yan Sanda Sun Yi Martani
Majalisar wakilai, a watan Fabrairun 2022, ta fara aiwatar da shirin kara mafi karancin cancantar ilimi na zabe a matsayin gwamna, dan majalisar jiha da na tarayya, zuwa akalla “matakin digiri na jami’a ko makamancinsa”.
Matakin karatun ministocin Tinubu
Lamba | Suna | Matakin karatu |
1 | Abubakar Momoh | Digiri na daya |
2 | Yusuf Maitama Tuggar | Digiri na biyu |
3 | Ahmad Dangiwa | Digiri na biyu |
4 | Hanatu Musawa | Digiri na biyu |
5 | Uche Nnaji | Digiri na daya |
6 | Betta Edu | Digirin digirgir |
7 | Doris Uzoka | Digiri na daya |
8 | David Umahi | Digiri na daya |
9 | Nyesom Wike | Digiri na biyu |
10 | Mohamed Badaru | Digiri na daya |
11 | Nasir El-Rufai | Digiri na biyu |
12 | Ekperikpe Ekpo | Digiri na biyu |
13 | Nkeiruka Onyejeocha | Digiri na biyu |
14 | Olubunmi Tunji-Ojo | Digiri na biyu |
15 | Stella Okotete | Digiri na biyu |
16 | Uju Ohanenye | Digiri na daya |
17 | Bello Mohammed Goronyo | Digiri na daya |
18 | Dele Alake | Digiri na biyu |
19 | Lateef Fagbemi | Digiri na biyu |
20 | Mohammed Idris | Digiri na biyu |
21 | Olawale Edun | Digiri na biyu |
22 | Adebayo Adelabu | Digiri na daya |
23 | Imaan Sulaiman-Ibrahim | Digiri na biyu |
24 | Ali Pate | Digirin digirgir |
25 | Joseph Utsev | Digirin digirgir |
26 | Abubakar Kyari | Digiri na dbiyu |
27 | John Enoh | Digiri na biyu |
28 | Sani Abubakar Danladi | Digiri na daya |
Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da zabebben ministan Tinubu da ya yi aiki da tsohon shugaba Jonathan
A bangarensa, Farfesa Mohammed Ali Pate wanda ɗan jihar Bauchi ne, ya samu damar shiga cikin jerin ministocin da Shugaba Tinubu zai naɗa cikin 'yan kwanakin nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanto sunayen mutane 28 da shugaban ƙasa ya aikawa majalisar domin a tantancesu.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, waɗannan wasu abubuwa ne guda 5 da ya kamata ku sani game da sabon ministan Tinubu, Farfesa Mohammed Ali Pate:
Asali: Legit.ng