An Sako Bokan Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Shi A Anambra

An Sako Bokan Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Shi A Anambra

  • Jami'an 'yan sanda a jihar Anambra sun sanar da sakin shahararren boka da masu garkuwa suka sace
  • An sace Chukwudozie Nwangwu ne a dakin otal a ranar 23 ga watan Yuli a karamar hukumar Anambra ta Arewa
  • Tun farko 'yan bindigan sun bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 300, amma ba a biya kudin ba kafin sake shi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Anambra - Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta sanar da samun labarin sakin shahararren boka da 'yan bindiga suka sace a jihar a makon da ya gabata.

Bokan mai suna Chukwudozie Nwangwu da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki an sace shi a dakin otal bayan bindige masu tsaronsa.

Shahararren boka ya shaki iskar 'yanci bayan masu garkuwa sun sake shi a Anambra
Shahararren Bokan Da Aka Sace Ya Shaki Iskar 'Yanci Bayan 'Yan Bindiga Sun Sake Shi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, DSP Tochukwu Ikenga shi ya bayyana sakin bokan a yau Asabar 26 ga watan Yuli a Awka, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Arewa Na Digan Jini Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Mata 23 Da Ma'aikatan Kamfani 10 a Zamfara

Rundunar ya bayyana yadda masu garkuwan suka bukaci a biya kudin fansa

Ikenga ya ce sun samu labarin cewa masu garkuwan sun saki bokan da safiyar yau Asabar 23 ga watan Yuli bayan shafe kusan mako guda a hannunsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng Hausa ta kawo muku labarin sace bokan a ranar 23 ga watan Yuli da misalin karfe 11:30 na dare a otal da ke karamar hukumar Anambra ta Arewa.

Ikenga ya ce masu garkuwan sun kira 'yan uwan bokan inda suka bukaci a biya kudin fansa har kusan miliyan 300, cewar The Nation.

Ikenga ya yi bayanin yadda aka sako bokan bayan shafe kwanaki

A cewarsa:

"Na samu labarin cewa ba su biya kudin fansar ba.
"Na kuma samu labarin cewa masu garkuwan sun sake bokan.
"Muna kokarin neman bayanai akan hakan don sanin ainihin abin da ya faru."

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka

Yan Sanda Sun Bazama Farautar Wadanda Suka Sace Boka A Jihar Anambra

A wani labarin, masu garkuwa da mutane sun sace wani shahararren boka a dakin otal a yankin Oba da ke karamar hukumar Anambra ta Arewa da ke jihar Anambra.

Bokan mai suna Chukwudozie Nwangwu da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki an sace shi ne a ranar 23 ga watan Yuli.

'Yan bindigan kafin sace bokan sun bindige masu tsaronsa guda biyu kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.