Sojoji Sun Cafke Tsohon Soja Mai Safarar Makamai Ga 'Yan Ta'addan Boka Haram a Bauchi
- Dakarun sojoji sun cafke wani baragurbin tsohon soja wanda yake safarar makamai ga ƴan ta'addan Boko Haram
- Dakarun sojojin cafke tsohon sojan ne a jihar Bauchi inda suka ƙwato makamai masu yawa a hannunsa
- Ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya ga dakarun sojoji a jihar Borno
FCT, Abuja - Hedkwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa an cafke wani tsohon soja mai safarar makamai da sauran kayan aiki ga ƴan ta'addan Boko Haram a ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da darektan watsa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar a ranar Juma'a 28 ga watan Yulin 2023, jaridar The Cable ta rahoto.
Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an cafke tsohon sojan ne a ranar 18 ga watan Yuli, a garin Boi cikin ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"A ranar 18 ga watan Yuli, dakarun sojoji sun cafke wani mai safarar bindigu a Boi cikin ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi."
"Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin korarren soja ne daga rundunar sojoji ta 5 Bde a Damasak. Dakarun sojojin sun ƙwato ƙananan bindigogi guda biyu, da harsasai 8 masu ƙaurin 9 mm."
Sojoji sun halaka ƴan ta'adda da dama
Haka kuma darektan watsa labaran ya bayyana cewa dakarun sojoji sun halaka ƴan ta'adda da dama a sassa daban-daban na ƙasar nan a cikin watan Yuli.
Buba ya bayyana cewa sama da ƴan ta'adda 700 waɗanda suka haɗa da ƙananan yara suka miƙa wuya ga dakarun sojoji a jihar Borno.
Buba ya ƙara da cewa wani ƙasurgumin ɗan ta'addan Boko Haram mai suna Ali, ya miƙa wuya a hannun dakarun sojoji a Dogumba cikin ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.
Sojoji Sun Halaka Yan Ta'adda 59
A wani labarin kuma, dakarun sojoji sun halaka ƴan ta'adda 59 a fafatawar da suka yi da su a cikin faɗin ƙasar nan.
Dakarun sojojin sun kuma ƙwato muggan makamai a hannun ƴan ta'addan tare da ceto mutane masu yawa da suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng