Yan Shi’a Sun Yi Zanga-zanga A Kaduna Don Nuna Bacin Ransu Kan Rashin Adalci Da Ake Wa El-Zakzaky

Yan Shi’a Sun Yi Zanga-zanga A Kaduna Don Nuna Bacin Ransu Kan Rashin Adalci Da Ake Wa El-Zakzaky

  • Kungiyar ‘yan shi’a a jihar Kaduna ta yi zanga-zangar lumana a manyan titunan birnin Kaduna don nuna damuwa kan rashin adalci da ake musu
  • An gano matasa da manya ‘yan kungiyar sun cika manyan titunan birnin a yau Juma’a 28 ga watan Yuli sanye da bakaken kaya na nuna alhini
  • Da yake Magana, kakakin kungiyar, Injiniya Yunusa ya ce dalilin zanga-zangar shi ne don nuna wa duniya halin rashin adalci da ake musu

Jihar Kaduna - Kungiyar ‘yan shi’a a Najeriya sun fita zanga-zanga a Kaduna kan rashin adalci da ake yi wa shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

‘Yan shi’an sun cika titin Ahmadu Bello a birnin Kaduna a yau Juma’a 28 ga watan Yuli inda suke dauke da kwalaye da suke nuna rashin jin dadinsu yadda ake muzantawa shugabansu.

Kara karanta wannan

Dalilan da Suka Jawo Babu Minista ko 1 Daga Kano, Filato da Legas a Sahun Farko

Kungiyar shi'a na zanga-zangar lumana a titunan Kaduna kan rashin adalci da ake nuna musu
Kungiyar Shi’a Na Zargin Hukumoni Da Nuna Rashin Adalci Ga Shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky. Hoto: Leadership.
Asali: Facebook

Kungiyar ta bayyana dalilin wannan zanga-zangar a Kaduna

A yayin zanga-zangar lumanar, matasan kungiyar sun yi shiga da bakaken kaya yayin da suke daga hannayensu sama, Leadership ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin kungiyar, Injiniya Yunusa Lawal Musa yayin hira da ‘yan jaridu ya ce suna wannan zanga-zangar ne don nuna rashin jin dadinsu akan abubuwan da ake musu.

Ya ce sun yi hakan ne a manyan titunan birnin Kaduna don sanar da mahukunta irin rashin adalci da ake musu da kuma shugabansu.

Kungiyar ta bukaci a bar kowa ya yi addinin da yake so

A cewarsa:

“Babban makasudin wannan tattaki shi ne don wayarwa mutane kai don su san irin rashin adalci da ake mana.
“Shugabanmu ya je kotu kuma ya yi nasara a dukkan korafe-korafen da ake a kansa, muna kira ga gwamnati da ta ba shi takardar shaidar fita waje don neman magani.”

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Matasan da Ba Ruwansu Sun Mutu Yayin da Jami'ai Suka Kai Farmaki a Jihar APC

Kungiyar ta kuma bukaci a bar kowa ya yi addininsa kamar yadda dokar kasa ta tanadar akan ko wane dan kasa, Stinomix ta tattaro.

Ta ce idan har gudanar da addinin bai saba wata doka ta cikin kundin tsarin mulki ba, to dole kowa a ba shi ‘yancin yin addinin da ya ke so.

‘Yan Shi’a Sun Caccaki El-Rufai Kan Rushe Musu Makarantun Da Asibiti

A wani labarin, Kungiyar Shi'a sun caccaki Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna kan rushe musu makarantu.

Kungiyar ta yi martanin ne bayan Hukumar Tsare-tsare da Raya Birane, KASUPDA ta rushe wasu daga cikin gine-ginensu.

Hukumar ta sanar fiye da mako daya tare da neman amincewar gwamnan domin aiwatar da rushe gine-gine a fadin jihar ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.