Sama Da 'Yan Najeriya 30,000 Ne Ke Aiki a Matatar Man Dangote, Kakakin Kamfanin Ya Yi Martani

Sama Da 'Yan Najeriya 30,000 Ne Ke Aiki a Matatar Man Dangote, Kakakin Kamfanin Ya Yi Martani

  • Hukumomin matatar man Dangote sun bayyana adadin ma’aikatan da ke aiki a kamfanin baki daya
  • Kakakin kamfanin na Dangote, ya ce a matatar akwai ‘yan Najeriya 30,000 duk da akwai ‘yan Indiya da China da ke aiki a wurin
  • Ya kuma bayyana cewa rahoton da ake yadawa cewa an dauki ‘yan kasar Indiya 11,000 a madadin 'yan Najeriya ba gaskiya ba ne

Matatar man Dangote ta karyata ikirarin cewa kamfanin na daukar ma’aikata ‘yan kasashen waje fiye da ‘yan Najeriya, kuma a halin yanzu akwai 'yan kasar Indiya 11,000 da ke aiki a wurin a maimakon ‘yan Najeriya.

Hukumar kula da matatar ta ce rahoton an yi shi ne kawai da nufin bata sunan kamfanin, amma ba wai zahirin abin da ke faruwa ba kenan a matatar.

An bayyana cewa 'yan Najeriya ne suka fi yawa a matatar man Dangote
An bayyana cewa 'yan Najeriya sama da 30,000 ne ke aiki a matatar man Dangote. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

'Yan Najeriya sun fi 'yan kowace kasa yawa a kamfanin na Dangote

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: An Bayyana Mutanen Da Shugaba Tinubu Zai Naɗa a Matsayin Ministoci Kwanan Nan

Legit.ng a wani rahoto da ta wallafa a baya, ta kawo bayanin da mai magana da yawun kamfanin na Dangote, Anthony Chiejine ya yi na cewa 'yan Najeriya sun fi 'yan kowace kasa yawa a matatar man.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chiejine ya ce, rahoton da wata kungiyar horar da mutane kan sana'o'i mai suna SASANET ta fitar na cewa matatar ba ta daukar ‘yan Najeriya da mutanen wasu kasashen na Afirka saboda rashin kwarewa ba gaskiya ba ne.

Ya kara da cewa an shirya rahoton ne da wata boyayyar manufa, saboda masu rahoton sun gaza bayyana adadin 'yan Najeriya da ke aiki a matatar.

'Yan Najeriya da ke aiki a matatar suna nuna kwarewa sosai

A wani rahoto da Business Day ta yi, an bayyana cewa yanayin yawan aikin da matatar man ke da shi ne ya sanya dole sai an nemo ma'aikata daga wurare daban-daban a fadin duniya da ke da kwarewa a fannoni da yawa.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Chiejine ya ce yayin da matatar man ta ke da ‘yan Najeriya sama da 30,000 da ke aiki a cikinta, akwai Indiyawa 6,400 da 'yan China 3,250 da su ma ke aiki a wurin.

Ya kara da cewa 'yan Najeriya da ke aiki a matatar sun nuna matukar kwarewa da basiri a ayyukan da suke gudanarwa.

Ya kuma nemi ‘yan Najeriya da su yi watsi da zarge-zargen da ake yi marasa tushe, su mayar da hankulansu kan tasirin matatar ga tattalin arziki da kuma jin dadin ‘yan kasa baki daya.

Gwamna Sule ya ce Dangote ne ya bashi shawarar fitowa takara ya kuma dauki nauyinsa

Legit.ng a baya ta kawo rahoton gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule, inda yake bayyana yadda Aliko Dangote ya ba shi shawarar fitowa takarar gwamna, sannan kuma ya dauki nauyinsa.

Sule ya ce ba zai taba mance irin hallacin da attajirin ya yi masa ba a rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng