Mahaifina Ba Zai Ba Ku Kunya Ba, Seyi Tinubu Ya Magantu Akan Shugabacin Bola

Mahaifina Ba Zai Ba Ku Kunya Ba, Seyi Tinubu Ya Magantu Akan Shugabacin Bola

  • Daya daga cikin 'ya'yan Shugaba Bola Tinubu, Seyi Tinubu ya bayyana cewa ya na da tabbacin shugaban ba zai ba da kunya ba
  • Seyi ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo inda ya ce irin shugaban da 'yan kasar ke muradi ya zo a wannan lokaci
  • Wannan na zuwa ne bayan cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi wanda ya jefa 'yan kasar a cikin wani hali

FCT, Abuja - Seyi Tinubu wanda ya kasance shi ne dan farin shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya na da tabbacin cewa mahaifinsa ba zai ba da kunya ba.

Seyi ya ce ya yi imanin cewa shugaban kasar a shirye ya ke wurin cika alkawuran da ya daukawa 'yan kasar.

Seyi Tinubu Ya Yi Magana Akan Mahaifinsa Ya Ce Ba Zai Ba Wa Najeriya Kunya Ba
Seyi Tinubu Ya Yabi Mahaifinsa Inda Ya Godewa 'Yan Kasar Akan Irin Goyon Bayan Da Suke Ba Su. Hoto: Pulse.
Asali: Facebook

Seyi Tinubu ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba 26 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fadi Hikimar Shugaba Tinubu a Cire Tallafin Fetur Tun Ranar Farko

Seyi ya godewa 'yan Najeriya kan irin goyon bayansu

Ya godewa 'yan Najeriya akan yadda suka yi imani da akalar gwamnatin Tinubu inda ya ba su tabbacin cewa sun samu shugaban da suke muradi, Pulse ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kalamai na Seyi na zuwa ne lokacin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki bayan cire tallafin mai.

A cikin faifan bidiyon, Seyi ya ba wa 'yan kasar tabbacin samun wakilci nagari daga mahaifin nasa, cewar Vanguard.

Ya ce tabbas shugaban ba zai ba da kunya ba

A cewarsa:

"Ina matukar gode muku saboda imanin da kuka yi akan shugaban kasar mu.
"Ina ba ku tabbacin Shugaba Bola Tinubu ba zai ba ku kunya ba.
"Irin imanin da muka yi a samun ingantaccen mulki ya zo, shugaban kasa da muke muradi ya zo yanzu, ina ba ku tabbaci."

Kara karanta wannan

Rikita-rikita Yayin Da Mata Ta Haifi 'Yan 4 Bayan Mijin Ya Yi Niyyar Zubar Da Cikin, Ya Nemi Taimako

Faifan bidiyon ya yadu sa'o'i kadan bayan Kungiyar Kwadago ta kasa ta shirya shiga yajin aiki idan ba a samu daidaito ba nan da kwanaki bakwai, cewar The Nation.

Tinubu Ya Gana Da Shugaban Kasar Benin, Talon A Abuja

A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Tinubu na ganawar sirri da shugaban kasar Benin, Patrice Talon kan yunkurin juyin mulki a Niger.

Shugaba Bola Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar kasashen ECOWAS ya nuna rashin jin dadinsa akan yunkurin juyin mulkin.

Talon, wanda ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 4:43 na yamma, ya kawo ziyara karo na biyu kenan a cikin makwanni biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.