Cire Tallafi: Jihohin Arewa Ne Suka Fi Shiga Matsi Kamar Yadda Sabbin Alkalluma Suka Nuna
- Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana jihohin da suka fi siyan mai da tsada a Najeriya tun bayan cire tallafi
- Hukumar ta ce wannan rahoto an bayyana shi ne bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi
- Jihohin Arewa sun fi fuskantar tsadar mai din wanda jihar Taraba ke kan gaba sai kuma jihar Yobe da kuma Kano
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa an samu karin farashin litar mai zuwa N545 a watan Yuni.
Karuwar ya kai kashi 210 idan aka kwatanta da yadda dan Najeriya ke shan litar mai akan N175 a watan Yuni na shekarar 2022.
Ainihin musabbabin tsadar mai din bayan cire tallafi
Hukumar ta fitar da wannan kiddigar ce bayan bincike tare da wallafa bayanan a shafinta kamar yadda Legit.ng ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsadar man fetur din ya samu dalili ne tun bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayu.
Hukumar ta fitar jerin jihohin da suka fi siyan mai tsada da kuma wadanda ke siya da araha.
Jihar Taraba ta fi kowa ce jihar siyan mai da tsada akan N562.86 akan kowa ce lita, sai kuma jihar Yobe akan N562.31 sai kuma Kano akan N561.82.
A daya bangaren, jihar Anambra ta fi kowa ce jiha siyan mai din da sauki akan N534.44 sai kuma jihar Ebonyi akan N535 da kuma jihar Oyo akan N537.43.
Jihohin da suka fi siyan mai da tsada:
1. Taraba - N562.86
2. Yobe - N562.31
3. Kano - N561.82
4. Gombe - N560.83
5. Borno - N557.14
6. Jigawa - N556.67
7. Abia - N552.73 8.
8. Adamawa - N551.25
9. Kogi - N550.83
10. Kaduna - N549.53
11. Zamfara - N549.09
Rashin Ciniki Da Sauran Tarin Matsalolin Da Masu Gidajen Mai Ke Fama Da Su Bayan Cire Tallafi
A wani labarin, tun bayan cire tallafin mai da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi a kasar, 'yan Najeriya suka shiga matsi na tsadar man fetur.
Shugaba Tinubu ya cire tallafin ne a ranar 29 ga watan Mayu yayin bikin rantsarwa a Abuja.
Masu gidajen mai sun koka kan yadda harkokin kasuwancinsu ke neman rugujewa tun bayan cire tallafin mai.
Asali: Legit.ng