Jerin Jihohin Da Suka Samar Da Ministoci 2 a Lokacin Mulkin Buhari
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada ministoci 44 a lokacin mulkinsa na biyu a shekarar 2019.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto, daga cikin ministoci 44 da aka nada, jihohi bakwai sun samu fiye da kujerar minista daya.
Bisa ga rahoton Vanguard, ga jerin sunayen ministocin, jihohi da kuma ayyukansu a kasa:
Jihar Anambra ta samu ministoci biyu
Chris Ngige – Jihar Anambra – Ministan kwadago da daukar ma'aikata
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sharon Ikeazor – Jihar Anambra – Karamin ministan muhalli
Buhari ya nada ministoci 2 daga jihar Bauchi
Adamu Adamu — Jihar Bauchi – Ministan ilimi
Ambasada Maryam Katagum – Jihar Bauchi – Karamar ministar kasuwanci
An nada ministoci 2 daga jihar Edo
Osagie Ehanire — Jihar Edo – Ministan lafiya
Clement Ike – Jihar Edo — Karamin ministan kasafin kudi
Jihar Kaduna ta samar da ministoci 2
Zainab Ahmed – Jihar Kaduna – Ministar kudi
Muhammad Mahmood – Jihar Kaduna – Ministan muhalli
Ministoci 2 daga jihar Kano
Sabo Nanono – Jihar Kano – Ministan noma da raya karkara
Bashir Salihi Magashi – Jihar Kano - Ministan tsaro
Buhari ya nada yan asalin jihar Kwara minista
Lai Mohammed – Jihar Kwara – Ministan labarai da al'adu
Gbemisola Saraki – Jihar Kwara – Karamar ministar sufuri
Jihar Lagas ta samu ministoci 2
Babatunde Fashola – Jihar Lagos – Ministan ayyuka da gidaje
Adeleke Mamora – Jihar Lagos – Karamin ministan lafiya
Na hannun damar Buhari da suka samu aiki bayan karewar wa'adin mulkinsu
A wani labarin, mun ji cewa Lai Mohammed wanda ya rike Ministan yada labarai da al’adu na Najeriya a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya samu aiki da wani kamfanin ketare mai suna Ballard Partners.
A wata sanarwa da Ballard Partners ya fitar a shafinsa na Twitter, an tabbatar da cewa Alhaji Lai Mohammed ya zama daya daga cikin abokan huldarsu.
Femi Adesina ya samu aiki bayan barin mulki
Hakazalika, tsohon kakakin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya samu aiki kwanaki kadan bayan sauka daga mulki.
Adesina ya bayyana cewa zai fara aiki a matsayin mataimakin shugaban kamfanin jaridar Sun daga ranar 1 ga watan Satumba, 2023.
Adesina ya rike kambun shugaban marubutan jaridar TheSun kafin daga bisani tsohon shugaban ƙasa Buhari ya naɗa shi a matsayin mai magana da yawunsa.
Asali: Legit.ng