APC Ta Maka Fitaccen Gwamnan PDP a Kotu Kan Nada Kansa Kwamishina

APC Ta Maka Fitaccen Gwamnan PDP a Kotu Kan Nada Kansa Kwamishina

  • Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Osun ta maka gwamnan jihar, Ademola Adeleke kan nada kansa mukami
  • Jam'iyyar ta shigar da karar ce kan zargin gwamnan da nada kansa kwamishinan ayyuka bayan kasancewarshi gwamna
  • Kotun ta kuma kalubalanci mataimakin gwamnan jihar, Kola Adewusi kan nada shi kwamishinan wasanni da bukata ta musamman

Jihar Osun - Jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta maka Gwamna Ademola Adeleke kan zargin nada kansa kwamishinan ayyuka.

Ana zargin gwamnan da nada kansa kwamishinan ayyuka a jihar bayan nada mataimakinsa na wasanni da bukata ta musamman.

APC Ta Maka Gwamnan PDP a Kotu Kan Nada Kansa Kwamishina
Jam'iyyar APC Na Zargin Gwamna Adeleke Da Nada Kansa Kwamishinan Ayyuka A Jihar. Hoto: Tori News.

Jam'iyyar ta maka PDP ne a kotu kan mukamin da gwamnan ya nada kansa

A karar da ta shigar a babbar kotun jihar, jam'iyyar ta kuma kalubalanci mataimakinsa, Kola Adewusi a matsayin kwamishinan wasanni da bukata ta musamman.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Zanga-Zanga Yayin da TUC Ta Ba Tinubu Makonni 2 Don Kammala Tattaunawa a Kan Cire Tallafin Mai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya bayyana wannan shirin nasa ne a ranar 19 ga watan Yuli inda jam'iyyar ta ankara da rashin dacewar hakan, PM News ta tattaro.

A kokarin sanin dacewar hakan, jam'iyyar ta bukaci bahasi daga kotun ganin yadda ta binciki kundin tsarin mulki inda ya haramta hakan.

Ta nemi bahasi kan hukuncin gwamna ya nada kansa kwamishina

Jam'iyyar ta kuma bukaci kotun ta yi bayani ko ya halatta gwamna mai ci ya rike wani mukami bayan na ofishinsa, cewar Premium Times.

Ta kawo misali a cikin kundin tsarin mulki a sashe na 192, inda ta ke bukatar kotun ta yi bayani ko ya dace a nada kwamishina ba tare an mika sunansa zuwa majalisar dokokin jiha.

Jam'iyyar ta kuma bukaci bahasi akan nada irin wadannan mukamai ba tare da an mika sunansu zuwa majalisar jihar ba don tantance wa da kuma bincike, Daily Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Dasa Kamarar CCTV a Gaban Kofarta, Ta Kama Makwabciya Da Ke Dauke Mata Kaya

MURIC Ta Zargi Gwamnan PDP Da Yi Wa Kungiyar CAN Aiki Yayin Nade-naden Mukamai

A wani labarin, Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta soki Gwamna Ademola Adeleke kan yiwa kungiyar CAN aiki a nade-naden mukamai.

Kungiyar ta fadi hakan ne bayan gwamnan ya bayyana jerin sunayen kwamishinoni da ya nuna fifiko na addini.

A jerin sunayen, kungiyar ta ce Adeleke ya fitar da jerin sunayen kwamishinoni 17 Kiristoci da Musulmai bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.