Kotu Ta Tasa Keyar Mutane 25 Gidan Kaso A Kano Kan Zargin Satar Fasahar Hukumar KAROTA

Kotu Ta Tasa Keyar Mutane 25 Gidan Kaso A Kano Kan Zargin Satar Fasahar Hukumar KAROTA

  • Wata kotun majistare a jihar Kano ta umarci tsare wasu mutane da ake zargi da damfara da kuma satar fasaha a gidan kaso
  • Wadanda ake zargin su 25 sun shiga hannu ne bayan hukumar KAROTA ta shigar da su kara kan zargin mallakar takardun bogi na hukumar
  • Mai Shari'a, Halima Wali ta ba da umarnin tsare su a gidan kaso tare da dage sauraran karar zuwa 27 ga watan Yuli

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Kotun majistare da ke zamanta a jihar Kano ta ba da umarnin tsare wasu mutane 25 a gidan gyaran hali da ake zarginsu da damfara da kuma satar fasaha.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata 25 ga watan Yuli bayan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa a Kano (KAROTA) ta shigar da su kara, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Hankula Sun Tashi Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai A Shagon Aski, 'Yan Sanda Sun Yi Martani

Kotu Ta Tsare Mutane 25 Gidan Kaso Kan Zargin Satar Fasaha Na KAROTA A Kano
Kotun Majistare Ta Tsare Wasu Mutane 25 Gidan Kaso A Kano Kan Zargin Mallakar Takardun Hukumar KAROTA. Hoto: Daily Post.
Asali: Facebook

Ana zargin mutanen da mallakar takardun bogi na KAROTA

Hukumar na zargin mutanen wadanda ba a bayyana inda suke zama ba da hadin baki da cuta tare da satar fasaha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai gabatar da kara, Tijjani Ibrahim tun farko ya fadawa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin a ranar 22 ga watan Yuli.

Ya ce a ranar da suka aikata laifin, an kama wasu daga cikinsu da rasit din bogi na hukumar KAROTA, cewar Punch.

Mai gabatar da karar ya ce aikata hakan laifi ne a dokar kasa da ya sabawa sashi na 97 da 393 da kuma 321 na dokokin jihar Kano.

An dage sauraran karar zuwa 27 ga wannan wata da muke ciki

Wadanda ake zargin ba su amince da tuhumarsu aka laifukan da ake yi ba, AllNews ta tattaro.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: NDLEA Ta Yi Gagarumin Kamu Na Buhuna 116 Na Tabar Wiwi a Jihar Kano

Lauyan wadanda ake zargi, Nazifi Rabiu ya bukaci kotun ta ba da belinsu kamar yadda sashe na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanadar.

Mai Shari'a, Halima Wali ta umarci tsare wadanda ake zargin a gidan gyaran hali tare da dage sauraran karar zuwa 27 ga watan Yuli don hukunci akan bukatar belin.

'Yan Karota Zasu Fara Kamen Masu Adaidaita Sahu A Jihar Kano

A wani labarin, Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa a Kano, KAROTA ta gargadi direbobin adaidaita da ke yawo babu sabuwar lambar hukumar.

Hukumar ta ce duk wanda suka gani a kan hanya ba tare da sabuwar lambar ba zai hadu da fushin hukumar.

Shugaban hukumar a jihar, Baffa Babba Danagundi shi ya bayyana haka ga manema labarai a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.