Hawaye Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai 3 A Shagon Aski, An Kwashe Su Zuwa Asibiti

Hawaye Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Bindige Wasu Dalibai 3 A Shagon Aski, An Kwashe Su Zuwa Asibiti

  • Wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne sun bindige wasu dalibai uku a Ilesa da ke jihar Osun
  • Wadanda aka harben, dalibai ne a Kwalejin Kiwon Lafiya ta jihar da ke Ilesa, da suka hada da mata biyu da namiji daya
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce dalibai na asibiti kuma suna samun sauki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Osun - Ana zargin 'yan kungiyar asiri da bindige wasu dalibai uku na Kwalejin Kiwon Lafiya (OSCOHT) da ke Ilesa a jihar Osun.

Lamarin ya faru ne a kwanan Amuta da ke kusa da makarantar a ranar Lahadi 23 ga watan Yuli.

'Yan Bindiga Sun Bindige Wasu Dalibai 3 A Shagon Aski
Wasu 'Yan Bindiga Da Ake Zargin 'Yan Kungiyar Asiri Ne Sun Bindige Dalibai 3 A Jihar Osun. Hoto: Tori News.
Asali: Facebook

Daliban sun shiga shagon ne don ba wa wayarsu wuta

Vanguard ta tattaro cewa daliban, namiji daya da mata biyu sun shiga shagon askin ne don saka wayarsu a caji inda maharan suka bude wuta a shagon.

Kara karanta wannan

FRSC Ta Yi Bayani Kan Hadarin Motar Da Ya Yi Sanadin Rasuwar Mutane 7 Da Jikkata 5 a Jigawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kwashi daliban zuwa asibitin koyarwa ta jihar da ke Osogbo don ba su kulawar gaggawa tare da ceto rayukansu.

Daga bisani an tattara yaran zuwa asibitin koyarwa na Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) don ci gaba da ba su ingantaccen kulawa na musamman.

'Yan sanda sun tabbatar da hakan, amma babu cikakken bayani

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu tabbacin ainihin abin da ya jawo wannan fada ba da ake zargin 'yan kungiyar asiri da aikatawa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Yemisi Opalola ta fadawa TheCable cewa daliban na asibiti kuma suna samun sauki kamar yadda ake bukata.

Sai dai ba ta ba da gamsassun bayanai game da harin ba da kuma wadanda ake zargin sun aikata, cewar Pulse.

Ta ce:

"Tabbas da gaske ne an harbi daliban kuma suna samun sauki a asibiti."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Ƙwararren Likita Yana Kan Aiki a Arewacin Najeriya

Ta katse wayar nan take ba tare da kara cewa komai ba ko kuma sauraran karin tambaya.

Rayuka Sun Salwanta A Wani Mummunan Hatsarin Mota A Jihar Osun

A wani labarin, wani mummunan hatsari ya yi ajalin mutane biyu akan hanyar Ife-Ondo da ke jihar Osun.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ita ta bayyana haka ta bakin Kwamandan shiyya, Agnes Ogungbemi a ranar Lahadin da ta gabata.

Hukumar ta ce hatsarin ya afku ne dalilin gudu ba bisa ƙa'ida ba da ɗaukewar burkin motar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.