Ana Cikin Jimami Yayin Da Babbar Mota Ta Yi Ajalin Basarake A Najeriya
- Wata babbar mota ta murkushe wani mai sarautar gargajiya har lahira a karamar hukumar Odo/Ota a jihar Ogun
- Marigayin Oba Abraham Bankole ya rasa ransa ne yayin sauka daga cikin adaidaita sahu akan hanyar Ota-Idiroko
- Kwamandan kula da dokokin hanya a yankin ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ganganci ne na direban
Jihar Ogun - Wani mai rike da sarautar gargajiya a karamar hukumar Ado-Odo/Ota a jihar Ogun ya rasa ransa dalilin hatsarin mota.
Marigayin Oba Abraham Bankole ya rasa ransa ne bayan wata babbar mota ta murkushe shi akan hanyar Ota-Idiroko a kokarinsa na saukowa daga adaidaita sahu.
Marigayin ya rasa ransa yayin saukowa daga cikin adaidaita sahu a bakin hanya
PM News ta tattaro cewa marigayin na kokarin sauka ne daga cikin adaidaita sahu lokacin da babbar motar ta murkushe shi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tabbatar da mutuwarsa nan take a kan babbar hanyar Ota-Idiroko kusa da majami'ar Winners.
Kwamandan Hukumar Kula da Dokokin Hanya (TRACE) a Sango Ota, Mista Adekunle Ajibade ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata hira da 'yan jaridu, cewar Vanguard.
Ajibade ya zargi direban da ganganci da kuma rashin kula a yayin tukin da ya jawo mummunan hatsarin.
Hukumar kula da dokokin hanya a yankin ta yi martani akan lamarin
Ya ce an wuce da gawar marigayin zuwa babban asibiti da ke Ota, Daily Post ta tattaro.
Ya ce tabbas lamarin da ya faru akwai gangaci a ciki wanda za a iya kare faruwar hakan.
A karshe ya shawarci direbobi da su guji tukin ganganci don gudun faruwar hakan a gaba.
Hatsarin Babbar Mota Ya Salwantar Da Rayuwar Wasu Tagwaye A Jihar Ogun
A wani labarin, ajali ya ci karo da wasu tagwaye masu shekaru 31 a duniya bayan kai ziyara wurin mahaifiyarsu a jihar Ogun.
Tagwayen sun gamu da ajalinsu ne bayan wata babbar motar daukar kaya ta murkushe su akan babur har lahira yayin dawowa daga ziyarar zuwa gida.
Lamarin ya afku ne a makon da ya gabata da ya hada da direban kabu-kabun, Wahab Lamidi, inda nan take shi ma ya ce ga garin ku nan.
Asali: Legit.ng