Hatsari ya salwantar da rayuwar wasu tagwaye bayan ziyarar Mahaifiyar su a jihar Ogun

Hatsari ya salwantar da rayuwar wasu tagwaye bayan ziyarar Mahaifiyar su a jihar Ogun

Kamar yadda rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch ta bayyana, wasu tagwayen juna Taiwo da Kehinde Animashaun, sun yi kacibus da ajali jim kadan bayan ziyarar Mahaifiyar su a gidan ta dake yankin unguwar Sango ta jihar Ogun.

'Karar kwana dake afkuwa babu shiri ta sanya wannan tagwaye masu shekaru 31 cikin rashin sani suka yi bankwana na karshe da mahaifiyar su, inda ajali ya katse ma su hanzari yayin komawa gidajen su.

Rahotanni sun bayyana cewa, tagwayen sun yi arangama da ajali ne a sakamakon hatsarin wata babbar motar daukan kaya da ya ritsa da su yayin da suke kan dan kabu-kabu.

Hatsari ya salwantar da rayuwar wasu tagwaye bayan ziyarar Mahaifiyar su a jihar Ogun

Hatsari ya salwantar da rayuwar wasu tagwaye bayan ziyarar Mahaifiyar su a jihar Ogun

Lamarin mai tattare da tsautsayi da ya afku a ranar Lahadin da ta gabata ya hadar har da direban kabu-kabun, Wahab Lamidi, inda nan take shima ya ce ga garin ku nan.

KARANTA KUMA: Rayuka 3 sun salwanta, Mutane 4 sun jikkata cikin wani mummunan hatsari a jihar Ogun

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, tagwayen na kan hanyar su ta dawowa daga ziyarar mahaifiyar su da misalin karfe 9.00 na dare, inda rai yayi ma su halin sa daura da wani wurin facin taya.

A sakamakon rashin bin ka'idar ajiye mota a gefen manyan hanya ya sanya tuni jami'an tsaro na 'yan sanda sun yi ram da Direban wannan babbar mota, Bisi Oluniyi, wanda ya ce ya dauko 'Bawon Rogo ne da nufin saukewa a wata gonar aladu dake yankin Oke-Aro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel