Albashin Aikin Gwamnati Zai Koma ‘Iyakar Kokarinka a Ofis Iyakar Kudinka’ a Wata

Albashin Aikin Gwamnati Zai Koma ‘Iyakar Kokarinka a Ofis Iyakar Kudinka’ a Wata

  • Abin da Gwamnatin tarayya ta ke shirin yi shi ne a rika biyan ma’aikaci albashin daidai aikin da ya yi
  • Folasade Yemi-Esan ta jaddada cewa ana kokarin fito da wannan tsari a Najeriya nan da shekarar 2025
  • A kokarin gyara aikin Gwamnati, Dr. Folasade Yemi-Esan ta nuna irin kokarin da ake yi a halin yanzu

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce ta na shirin kawo tsarin da zai jawo a rika sallamar duk wani ma’akaci daidai da kwazon da ya nuna a wurin aikinsa.

A safiyar Laraba, This Day ta rahoto shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan ta sake dauko wannan magana a garin Abuja.

Yayin da ta ke magana da manema labarai a jiya. Folasade Yemi-Esan ta shaida masu inda aka kwana a kan aikin gwamnati da shirin da ake yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Karawa Duk Ma’aikacin Gwamnati Kudi a Dalilin Tsadar Man Fetur

Gwamnatin Tarayya
Rantsar da Sakataren Gwamnatin Tarayya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A nan aka ji shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayyan ta na cewa an sanar da manyan sakatarori za a rika duba kwazo kafin ayi karin matsayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nan da shekarar badi ta 2024, gwamnatin tarayya ta na so a kawo gyara a yadda ake daukar aiki da biyan ma’aikata da duk wani abin da ya shafi aikin.

Ana so a gyara aikin gwamnati

Kafin yanzu aka fara kawo wannan magana a Najeriya, gwamnati ta na so nan da 2025, albashin da ma’aikaci zai samu ya zama daidai da aikinsa.

A karkashin tsarin SMAT-P, Yemi- Esan ta ce sun horas da ma’aikata 6, 007, sannan ana ta shigo da fasahohin zamani da nufin inganta aikin gwamnati.

Jaridar ta ce Yemi-Esan ta yi bayanin yadda aka horar da ma’aikata fiye da 16, 000 a shekarar nan.

Za a bankado marasa gaskiya

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Albani Ya Hango Janye Tallafin Man Fetur Shekaru 9 da Suka Wuce

A kokarin da ake yi na ganin an magance rashin gaskiya a aiki, jami’an gwamnatin kasar ta ce sn gano takardun daukar aiki na bogi fiye da 1, 600.

Sannan an dakatar da wasu ma’aikata da aka samu su na aika-aika da manhajar IPPIS da ake amfani da ita wajen biyan albahin ma’aikata a kasar.

Bayan haka, akwai manyan jami’ai 3, 657 da hukumar ICPC ta ke bincike a kan su domin ba a same su a ofis ba a lokacin da ake tantance ma’aikata.

Najeriya a taron Duniya

Sanata Kashim Shettima ya tafi kasashen waje a karon farko bayan shiga ofis, an ji labari Mataimakin shugaban kasan zai wakilci Bola Tinubu a ketare.

Shettima ya isa tun tuni, ya na halartar wasu taro da za ayi a Rome da St Petersburg.Akwai jami’an gwamnatin tarayya da su ke masa rakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng