Cire Tallafin Man Fetur: Gwamnonin Kwara Da Ogun Sun Amince Da Rabon N10,000 Ga Ma'aikata

Cire Tallafin Man Fetur: Gwamnonin Kwara Da Ogun Sun Amince Da Rabon N10,000 Ga Ma'aikata

  • Dapo Abiodun da AbdulRahman AbdulRasaq na jihohin Ogun da Kwara sun amince da rabon tallafin N10,000 ga ma'aikatan jihohinsu
  • Gwamnonin biyu na jam'iyyar APC sun sanar da cewa tallafin ba ma'aikata kaɗai za a rabawa ba, har da ɗalibai da ƴan fansho
  • Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya kuma amince da biyan kuɗin alawus na ma'aikatan lafiya a jiharsa

Abeokuta, Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun da takwaransa na jihar Kwara AbdulRahman AbdulRasaq sun sanar da riƙa tura N10,000 duk wata ga ma'aikatan a jihohinsu.

Hakan na ƙunshe ne a cikin labaran tashar AriseTV na ranar Talata, 25 ga watan Yuli wanda aka sangaa shafinta na Youtube, inda tace gwamnonin sun amince da rabon tallafin kuɗi ga ma'aikata a jihohinsu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: Jami'ar Najeriya Za Ta Gwangwaje Ma'aikata Da Dalibanta Da Kayan Tallafi

Gwamnonin Kwara da Ogun sun amince da rabon tallafin N10k ga ma'aikata
Gwamnonin sun ce tallafin zai rage radadin cire tallafin man fetur Hoto: Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Gwamnan APC Abiodun ya amince da biyan kuɗin alawus na ma'aikatan lafiya

Abiodun da AbdulRasaq gwamnoni ne waɗanda aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyya All Progressives Congress (APC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abiodun ya kuma amince da biyan kuɗin alawus ga ma'aikatan lafiya a faɗin jihar.

AbdulRasaq, ya bayyana cewa ma'aikatan za su fara amsar tallafin ne a wannan watan na Yuli, har zuwa lokacin da za a yi duba kan mafi ƙarancin albashin da su ke amsa, inda ya ƙara da cewa hakan zai taimaka musu wajen rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Gwamna AbdulRasaq ya kuma buƙaci ma'aikatan da su ci gaba da amfani da tsarin zuwa wurin aiki sau uku a sati.

Rabon tallafin N10,000 ba ma'aikatan jihar kawai za a yi wa ba, har da ɗalibai da ƴan fansho.

Ku kalli bidiyon nan ƙasa:

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Bankaɗo Badaƙalar Maƙudan Kuɗi, Ya Ceto Biliyan N1.2 Daga Ma'aikata

Litar Man Fetur Za Ta Dawo N50 - Fitaccen Malami

A wani labarin kuma, wani fitacccen malamin addinin Kirita ya hango sauƙi na nan tafe ga talakawa a Najeriya a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Prophet Elijah Bamidele, na cocin Christ House of Prayer and Deliverence ya tabbatar da 'yan Najeriya na shan wahala a mulkin Shugaba Tinubu. Sai dai, malamin addinin ya bayyana cewa bayan wuya daɗi na tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng