“Fetur Sai Wata Rana”: Matashi Ya Tuka Babur Mai Cin Mutum 7 Da Ke Aiki Da Lantarki, Ya Burge Yan Najeriya
- Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wasu matasa biyu suna tuka wani babur mai cin mutum bakwai
- Ga dukkan alamu, matasan suna jin dadin yanayin yayin da suke karade gari kan babur din ba a saba gani ba
- Wasu masu kallo sun yi ba a inda suka ce babur din zai dace da zama madadin motoci, musamman da tsadar man fetur a Najeriya
Wani bidiyon TikTok mai ban mamaki ya ja hankalin masu kallo da dama, yayin da yake dauke da kujerun zama na mutum bakwai kuma yana aiki ne da lantarki. An gano wasu matasa biyu a kansa.
Alamu ya nuna matasan na jin dadin rayuwarsu yayin da suke tuka babur din a titi, an shirya kujerun mutum bakwai bi da bi a tsakanin babur din.
Wani mutum ya tuka babur mai cin mutum 7 da ke aiki da lantarki
Wasu daga cikin mutanen da suka yi martani a bidiyon sun bayyana cewa babur din shine mafita ga mutanen da son samun rarar kudi a kan man fetur, wanda ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sauran jama'a sun yaba ma fasahar da ya kirkiri wannan babur din, wanda ke ba mutane da dama jin dadin tafiya a kai.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya samu dubban mutane da suka kalle shi da 'likes' masu yawan gaske a TikTok.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@faitheminobowa ta yi martani:
"Magana ta gaskiya wannan zai yi wa yan Najeriya amfani sosai a yanzu ina ganin akwai bukatar mu yada wannan har sai ya kai gare su."
@joyDhot ta ce:
“Idan Batirin Ya Kare Fa?” Dan Najeriya Ya Mayar Da Motar Bas Zuwa Mai Amfani Da Wutar Lantarki, Ya Ce Ya Rabu Da Wahalar Mai
"Babu karya. Muna bukatar wannan a Lagas."
@Nancyblack ta rubuta:
"Irin wannan muke bukata yanzu a Najeriya."
@nikkyB02 ma ta yi martani:
"Kamfanin zai yi ciniki sosai fa a Najeriya."
@User8421789799346:
"A wani hanyar. ya tafi."
Cire tallafin mai: Kungiyar kwadago ta ba Tinubu makonni 2 ya yi wani abu
A wani labarin, mun ji cewa an baiwa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sabuwar sanarwa dangane da tattaunawa a kan cire tallafin man fetur.
Yayin da yan Najeriya ke jiran sakamakon tattaunawa tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya kan matakan rage radadin da cire tallafin man fetur , kungiyar TUC ta yi barazanar fara yajin aiki na gama gari.
Asali: Legit.ng