“Zai Iya Tsawon Awanni 8”: Dan Najeriya Ya Mayar Da Motar Bus Zuwa Mai Amfani Da Wuta, Ya Kai Shi Gidan Caji

“Zai Iya Tsawon Awanni 8”: Dan Najeriya Ya Mayar Da Motar Bus Zuwa Mai Amfani Da Wuta, Ya Kai Shi Gidan Caji

  • Wani matashi ya wallafa bidiyon wata mota da ke caji a wani gidan caji bayan an sauya injin dinta
  • An gano bas din tsaye a gaban mita yayin da aka makala tiyonta a gefen motar domin caja ta da wutar lantarki
  • Yan Najeriya da dama da suka kalli bidiyon sun tambayi yadda za a iya sauya injin dinsu mai aiki da man fetur zuwa lantarki don rage tsadar hawa mota

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutum ya wallafa wani bidiyo na yar karamar motar bas da aka sauya ta daga injin mai amfani da mai zuwa mai amfani da wutar lantarki.

An paka motar a gaban mita kamar dai yadda ake yi a gidan mai. Wata murya da ke tashi ta karfafawa mutane gwiwar mayar da injinan motocinsu zuwa masu amfani da wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Soyayya Ruwan Zuma: Bidiyon Yadda Amarya Ta Kama Wasa Da Angonta a Wajen Budar Kansu Ya Dauka Hankali

Mota mai aiki da wutar lantarki
“Zai Iya Tsawon Awanni 8”: Dan Najeriya Ya Mayar Da Motar Bus Zuwa Mai Amfani Da Wuta, Ya Kai Shi Gidan Caji Hoto: @charleyman8
Asali: TikTok

Tashar cajin motoci da wutar lantarki

An jona cajin da ke jikin mitan a wajen cajin da ke gefen motar bas din. Wani katon allo da ke gaban gidan cajin ya nuna cewa ana sanya kowani kilowatt na wuta a kan N150.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu mutane sun taro a wajen motar da ke caji don daukar bidiyon wannan sabuwar fasahar. A wani bidiyon, wani mutum (@charleyman8) ya yi bayanin cajin nawa motar za ta iya sha a kowani lokaci, yana mai bayyana lokacin tsakanin awanni bakwai da takwas.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

user9249885215630 ya ce:

"Eh lokaci ya yi da za mu fara amfani da motoci masu aiki da wutar lantarki."

user5815598716328 ya tambaya:

"Idan aka haramta motoci masu caji a nija yaya za ka yi?"

realben_nc4a ya ce:

"Kada ka manta ka siya pôwêr bank ka hada dan uwa, kada ka ce ban fadi nawa ba."

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

obichidubemfrankl ya tambaya:

"Me ake bukaa don sauya shi kuma yaya karkonsa yake?"

Cosmos ya ce:

"Ita wasa har sai batir dinka ya yi kasa kamar wayar Iphone a kan hanya da baida kyau."

Legit.ng ta zanta da wani mutum da ya mallaki abun hawa mai suna mallam Abubakar don jin ta bakinsa game da sauya motoci zuwa masu amfani da wutar lantarki.

Malam Abubakar ya ce:

“A matsayina na mai motar hawa da ke amfani da man fetur ina ganin idan har na samu dama zan sauya motata zuwa mai amfani da lantarki.
“Dalilina kuwa shine motoci masu amfani da lantarki za su fi saukin harka, sa’annan zai zamana akwai wuraren caji kamar yadda ake da gidajen mai sannan ba za su zamo da tsada kamar man fetur ba.
“Kuma hakan zai sa a inganta wutar lantarki. Zai kuma sa mutane su samu rara wajen siyan sauran kayan amfani tunda ba mota kadai mutum zai dunga kashewa kudi ba yadda man fetur ke kara tsada kullun.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Tuka Amala Da Na'ura Maimakon Muciya Ya Tashi Kan Yan Mata

Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30

A wani labari da daban, mun kawo cewa kyawawan hotunan adaidaita sahu masu aiki da lantarki wanda kamfanin Phoenix Renewable Limited ya kera a Maiduguri sun yadu a shafukan soshiyal midiya.

Hadaddun hotunan adaidaita sahun wanda ake yiwa lakabi da Keke Napep ya sanya yan Najeriya da dama tofa albarkacin bakunansu sannan sun bukaci gwamnati da ta tallafawa kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng