Bidiyon Rashin Da’a Ga Musulunci: MURIC Ta Caccaki Davido, Ta Bukaci DSS Da Ta Gayyaci Mawakin

Bidiyon Rashin Da’a Ga Musulunci: MURIC Ta Caccaki Davido, Ta Bukaci DSS Da Ta Gayyaci Mawakin

  • Ana ci gaba da yin Allah wadai da bidiyon rashin da'a ga Musulunci da mawakin kudu, Davido ya saki
  • A wannan karon, kungiyar kare hakkin musulmi ta bukaci hukumar DSS da ta kama mawakin a kan bidiyon
  • Shararren mawakin Najeriyan ya sha suka a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli, bayan ya saki waki bidiyo main suna ‘Jaye Lo' kuma tuni ya sauke bidiyon

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gayyaci shahararren mawakin nan na Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido da Logos Olori kan bidiyonsu wanda ya nuna rashin da'a ga addinin Islama.

Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya yi kiran a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, a Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abin Duniya Ya Jawo Rigima Tsakanin Mashahurin ‘Dan Kasuwan Najeriya da Yaransa

MURIC ta nemi DSS ta gayyaci Davido
Bidiyon Rashin Da’a Ga Musulunci: MURIC Ta Caccaki Davido, Ta Bukaci DSS Da Ta Gayyaci Mawakin Hoto: Professor Ishaq Akintola, @davido
Asali: Facebook

Davido da Logos Olori, wanda ainahin sunansa Olamilekan Emeka Taiwo sun sha suka mai yawan gaske a karshen mako bayan sun saki bidiyon wani waka ‘Jaye Lo’ a intanet.

Muna kira ga hukumar tace fina-finai da bidiyoyi da ta haramta wakar 'Jaye Lo’, MURIC

A bidiyon, an gano Logos Olori yana sallah a kan darduma kafin ya fara waka da rawa, yayin da ya zauna a kan lasifikar da aka daura a kan wani gini da ya yi kama da masallaci, rahoton Within Nigeria.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Muna jan hankalin jami’an hukumar tsaro na farin kaya da su gayyaci matasan biyu don amsa tambayoyi domin su yi bayanin dalilin da yasa suka zabi samar da bidiyon waka da ka iya haddasa tashin hankali a Najeriya.
"A cikin irin haka, muna gayyatar hukumar kula da kafafen watsa labarai (NBC) da hukumar tace fina-finai da bidiyoyi na kasa (NFVCB) da ta gaggauta haramta bidiyon wakar na rashin hankali mai taken ‘Jaye Lo’ daga Logos Olori.”

Kara karanta wannan

Za su ji a jikinsu: Davido ya yiwa Musulmai martanin gatsali bayan jawo hankalinsa ga bidiyon yiwa sallah izgili

Ya kara da cewar ya zama dole wadannan hukumomi da aka lissafa su shiga aiki nan take daga lokacin da aka ja hankalinsu zuwa ga lamarin da ka iya kawo rashin zaman lafiya a kasar.

Davido ya goge bidiyon da ya haddasa cece-kuce tsakaninsa da Musulmai

A gefe guda, mun ji cewa daga karshe mawaki Davido ya sauke bidiyon waka da ya sanya a shafinsa wanda ya haddasa cece-kuce a tsakanin musulmai.

Musulmai dai sun ga cewa mawakin bai kyauta masu ba sakamakon nuno su da aka yi suna wasa da sallah a bidiyon waka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng