Kasashe 10 Da Suka Fi Samun Hauhawa Farashin Abinci Tsakanin Watan Maris Zuwa Yunin 2023
- Kasar Najeiya ta tsallake bayan Bankin Duniya ta fitar da jerin kasashe 10 da suka fi tsadar kayan abinci
- Bayan cire tallafi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a watan Mayu, ya kuma bar Naira ta yi yawo a kasuwa
- Wadannan matakai na Bola Tinubu sun jawo tashin farashin kaya musamman abinci da kuma harkokin sufuri
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Yayin da kasashe da dama ke fuskantar hauhawan farashin kaya, abin da yafi daukar hanakali shi ne tsadar abinci.
Bankin Duniya ta bayyana cewa kasashe na fama da tashin farashin kayayyaki saboda fadan da ake tsakanin Russia da Ukraine da sauran matsaloli.
A dalilin haka, kasashe da dama na daukar matakai don shawo kan matsalar da kuma samar da sauki ga mutanen kasarsu, Legit.ng ta tattaro.
Tinubu ya cire tallafi wanda ya kara farashin kaya a kasar
Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin mai da kuma barin farashin Naira ta yi yawo a kasuwa wanda ya kara hauhawan farashin kaya da sufuri a kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Duk da haka Najeriya ba ta daga cikin kasashen da suka fi fuskantar matsalar hauhawan farashi musamman na abinci a duniya, kamar yadda Bankin Duniya ta bayyana.
Har ila yau, Bankin Duniya ta bayyana jerin kasashen da suka fi samun matsalar hauhawan farashin abinci daga watan Maris zuwa Yuni na shekarar 2023.
Kasashe 10 da suka fi samun matsalar tashin farashin abinci:
1. Venezuela - 414%
2. Lebanon - 304%
3. Zimbabwe - 256%
4. Argentina - 118%
5. Suriname - 71%
6. Egypt - 66%
7. Sierra Leone - 56%
“A Wannan Marran”: Peter Obi Ya Yi Martani Ga Ma’aikaciyar Otel Da Ta Mayar Da Miliyan 55 Da Ta Tsinta
8. Turkey - 54%
9. Ghana - 52%
10. Haiti - 48%
Farashin Kayayyaki: Jerin jihohin Najeriya 10 Da Suka Fi Fuskantar Matsalar A 2023
A wani labarin, masana sun yi hasashen samun tashin kayayyaki musamman na abinci a Najeriya nan ba da dadewa ba tun bayan hawan Shugaba Tinubu karagar mulki.
Masanan sun ce irin matakan da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke dauka su ne za su kawo tashin farashin kayayyaki musamman ma na abinci a kasar..
Matakan sun hada da cire tallafin man fetur da kuma karyewar darajar Naira a kasuwa, a cikin labarin akwai jerin jihohin da suka fi fuskantar wannan matsalar a Najeriya.
Asali: Legit.ng