Bola Tinubu Ba Zai Je ba, Kashim Shettima Zai Wakilci Shugaban Najeriya a Rasha
- An gayyaci Najeriya zuwa taro a Italiya da Rasha, amma shugaban kasa ba zai samu zuwa ba
- Kashim Shettima zai wakilci Bola Ahmed Tinubu, jirgin fadar shugaban Najeriya ya tashi tun jiya
- Mataimakin shugaban kasan da jami’an gwamnatin tarayya za su shafe kusan kwanaki 7 a ketare
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima zai wakilci Mai girma Bola Ahmed Tinubu a wasu taro da za ayi a kasashen Italiya da Rasha.
Sanata Kashim Shettima zai halarci taron da za a yi a birnin Rome a Italiya da wani a St Petersburg a kasar Rasha kamar yadda aka sanar a jawabi a jiya.
Darektan yada labarai na ofishin Mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola, ya nuna Shettima ya bar Najeriya tun Lahadi, zai sauka a babban birni Rome.
Kashim Shettima ya na Italiya
The Cable ta rahoto Mista Abiola yana mai cewa mataimakin shugaban kasar zai kasance tare da sauran shugabannin Duniya a taron STM da za ayi a Rome.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shettima ya tabbatar a Facebook cewa sun isa Italiya. An shirya zaman ne kan harkar abinci, za a dauki kwanaki biyu daga Litinin zuwa Laraba ana taron.
Sanarwar ta kara da cewa Sanata Shettima zai jagoranci wani zama da za ayi mai taken “Dabarun samar da kudi wajen kawo sauyi a harkar abinci a Najeriya.”
Daga Italiya sai kasar Rasha?
An rahoto Abiola ya ce kungiyar abinci ta Duniya watau FAO da ke karkashin majalisar dinkin Duniya, da irinsu IFAD da WFD ne su ka shirya wannan taro.
Ana gama wannan taro kuma Shettima zai wuce birnin St. Petersburg a Rasha domin ya wakilci shugaban kasa wajen taron hadin-kan Rasha da nahiyar Afrika.
Shi kuma wannan taro zai dauki tsawon kwanaki hudu, sai ranar Asabar za a kammala.
Mataimakin shugaban Najeriyan zai hadu da sauran shugabannin kasashen Rasha da na nahiyar Afrika wajen ganin yadda za a bullowa matsalolin kasar nan.
Premium Times ta ce za a tattauna a kan harkar kasuwanci tsakanin jami’an gwamnatocin Najeriya da Rasha, bayan nan tawagar za ta dawo garin Abuja.
Sauran jami’an gwamnati su na cikin wadanda za su yi wa wakilin shugaban kasar rakiya.
Nadin Ministoci a Najeriya
Ku na da labari cewa Sanatoci su na sauraron Shugaban kasa a daidai lokacin da kwanaki biyar su ka ragewa Bola Tinubu ya fito da Ministocin tarayya.
Har yanzu sunayen wadanda za su iya zama Ministoci bai bar Aso Rock ba, ana ta ‘yan canje-canje, ana batun cewa an cire sunayen wasu mutum hudu.
Asali: Legit.ng