Majalisar Dattawa Ta Tona Asirin Wadanda Ake Bin Su Kudin Wuta Mai Yawa a Najeriya
- An bayyana wasu cibiyoyi da hukumomin gwamnati a matsayin manyan wadanda kamfanonin rarraba kudin lantarki ke bi bashi a Najeriya
- Adadin bashin da ake bin su ya fara zama rakai da wahala ga DisCos don gudanar da ayyukansu na yau da kullum
- Ministan wutar lantarki ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya na ba da tallafin wutar lantarki sosai a Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin wutar lantarki Sanata Gabriel Suswam ya bayyana sunayen wadanda ake bin su manyan kudade na bashin wutar lantarki a Najeriya.
Yayin da yake magana a wata tattaunawa da Mista Abubakar Aliyu, karamin ministan wutar lantarki a Abuja, Suswan ya bayyana cewa wadanda suka fi cin bashin DisCos su ne gwamnatocin jihohi, cibiyoyin ilimi da barikin soja, in ji jaridar The Nation.
Basusukan da DisCos ke bin hukumomin gwamnati, ya yi tasiri sosai wajen saka hannun jari a kamfanonin rarraba wutar lantarkin da ma inganta ayyukansu.
Da yake ba da shawarin mafita kan lamarin, Suswam ya ba da shawarar cewa ma'aikatar kudi ta cire wani kaso daga kudin gwamnatoci, ma'aikatu, hukumomi da sauransu tare da biyan bashin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Minista ya ce wutar lantarki a Najeriya ya fi ko ina araha a duniya
Da yake mayar da martani, Aliyu ya bayyana cewa idan aka kwatanta da sauran kasashe, kudin wutar lantarki a Najeriya ta fi ko ina araha a duniya.
Sai dai ya yi mamakin yadda duk da haka, Najeriya ce ta fi kowacce kasa yawan wadanda ake bin bashin kudin wutar lantarki, rahoton PM Parrot.
Aliyu ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta saka wa Najeriya tallafin wutar lantarki sosai, wanda hakan ya sa kudin ya zama mafi araha a duniya.
Domin tabbatar da ikirarinsa, ministan ya yi yunkurin kwatanta farashin wutar lantarki a Najeriya da kasashen makwabta a Afirka.
Yace:
"Misali, yayin da farashin wutar lantarki a Najeriya ya ke 15% a kowace kilowatt, 42% ne a Jamhuriyar Nijar, 23% ne a Jamhuriyar Benin, 25% ne a Mali, 28% ne a Senegal, 27% ne a Burkina Faso da dai sauransu."
Duk da rashin wuta a cikin gida, Najeriya na bin Nijar, Benin da Togo bashin kudin wuta
A wani labarin, Najeriya na bin jamhuriyar Nijar, Benin da Togo kudaden da suka kai Naira biliyan 5.86 a shekarar 2020 na wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta nemi kasashen su biya.
A rahoton da Daily Trust ta fitar, an ce Najeriya a harkallar wutar lantarki da kasashen, ta nemi su biyu N16.31bn na wutar da ta ba su a shekarar ta 2023.
Asali: Legit.ng