Ko an ki ko an so: Akpabio Zai Fito da Sunayen Ministoci a Makon da Za a Shiga

Ko an ki ko an so: Akpabio Zai Fito da Sunayen Ministoci a Makon da Za a Shiga

  • Ya zama dole a cikin makon gobe, Bola Ahmed Tinubu ya fito da wadanda yake so su zama Ministoci
  • Idan an aika sunayen wadanda za a ba mukaman, daga nan za ayi haramar tantance su a Majalisa
  • Shugaban kasa da Gwamnoni ba su isa su wuce Asabar ba su fitar da Ministoci da Kwamishinoni ba

Abuja - Bisa dukkanin alamu, a makon nan da za a shiga, Godswill Akpabio zai fitar da sunayen wadanda ake so a ba kujerar Ministoci.

Rahoton Punch ya nuna za a san wadanda Bola Ahmed Tinubu ya zaba domin ya yi aiki da su a majalisar FEC nan da awanni masu zuwa.

Wannan ne makon karshe ga sabon shugaban kasar yake da shi domin fitar da Ministocinsa.

Bola Tinubu
Bola Tinubu bai nada Ministoci ba Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulki ya wajabta fitar da Ministoci da Kwamishononi a matakan jihohi da tarayya cikin kwana 60.

Kara karanta wannan

Su waye ministocin Tinubu? Jigon siyasa ya fadi dalilin jinkirin nada ministoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai an tantance su a Majalisa

Ma’anar hakan shi ne ga shugaban kasa da sababbin Gwamnoni 28 da aka zaba a bana, dole za su sanar da wadanda za a tantance kafin Asabar.

Da zarar an fitar da sunayen, sai a fara shirin tantance su a majalisar dattawa da dokoki. Wani Sanata ya ce hakan zai dauki kusan mako guda.

Legit.ng Hausa ta na sa ran tsakanin Talata, Laraba ko Alhamis da Sanatoci su ke yin zama, a karanto wasikar shugaba Bola Tinubu game da batun.

Majiyoyi daga majalisar tarayya sun ce wasikar da shugaban kasa ya aikowa shugaban majalisar dattawa ta iso tun a makon da ya gabata.

A cewar majiyar, a makon nan da za a shiga, Akpabio zai karanto abin da takardar ta kunsa bayan an yi wasu ‘yan kwaskwarima a mintin karshe.

Kara karanta wannan

An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

Me ya jawo bata lokaci?

“Shugaban majalisar dattawa ya samu jerin Ministocin a makon jiya, amma lokaci bai yi da zai fito da shi, shiyasa ya boye.
Mafi muhimmanci, an samu wasu ‘yan gyare-gyare a karshe. Shugaban majalisa ya yi zama da Tinubu kan batun a makon jiya."

- Majiya

Mutanen Najeriya za su sha mamaki

Wani da ya san halin da ake ciki ya ce jama’a za su yi mamaki idan su ka ji sunayen wadanda aka zaba, ya ce za ayi fatali da wasu ‘yan siyasa.

"A makon nan za a fitar da sunayen Ministoci. Kuma abin da zan iya fada maka shi ne abin zai girgiza ‘yan Najeriya, guguwar Tinubu kenan."

- Wata majiya

Daukar aiki a gwamnatin tarayya

An ji labari Sanatan Kudancin Benuwai kuma tsohon Minista, Abba Moro ya ce a daina cusa shekaru a sharadin neman aiki da ake yi a Najeriya.

A majalisar wakilai, Hon. Francis Waive ya ce a halin da aka samu kai, dole a cigaba da daukar aikin gwamnati domin rage masu zaman kashe wando.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng