Yan Bindiga Sun Sace Mutum Hudu Cikin Wani Kauye a Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Sace Mutum Hudu Cikin Wani Kauye a Jihar Zamfara

  • Ƴan bindiga sun bi cikim dare sun yi awon gaba da wasu mutum huɗu a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan sun mutanen ne waɗanda iyalai ne a wajen wani babban ɗan siyasa a.ƙauyen Danbaza inda sace mutanen
  • Miyagun sun nemi da a basu kuɗin fansa har N80m kafin su sako mutum huɗun waɗanda uku daga cikinsu mata ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Miyagun ƴan bindiga sun sace mutum huɗu a ƙauyen Danbaza a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kira waya jim kaɗan bayan sace mutanen inda suka nemi da basu tsabar kuɗi har N80m a matsayin kuɗin fansa, kafin su sako mutanen, rahoton TVC News ya tabbatar.

Yan bindiga sun sace mutum hudu a jihar Zamfara
Yan Bindigan sun zo ne da niyyar sace dan siyasan Hoto: Theguardian.com
Asali: UGC

Mutanen da aka sace ɗin dai, mata ne guda uku da wani matashi guda ɗaya waɗanda ƴaƴa ne da jikar wani ɗan siyasa a ƙauyen.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Ƴan bindigan dai sun dira a ƙauyen ne da misalin ƙarfen 3:00 na dare inda kai tsaye suka wuce gidan ɗan siyasan da niyyar su sace shi, sai dai basu tarar da shi ba saboda baya nan ya tafi a duba lafiyarsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun sace biyu daga cikin ƴaƴansa, babban ɗansa da jikarsa. Ƴan bindigan sun kuma lakaɗawa wasu dukan tsiya saboda sun ƙi nuna musu gidan wani mai siyar da kayan abinci a ƙauyen.

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton dai, ƴan bindigan na ci gaba da riƙe mutanen a hannunsu, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yadda za a sako su.

Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin

Rundunar ƴan sandan jihar ta hannun kakakinta, Yazid Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa har yanzu ba a gaya musu adadin yawan mutanen da aka sace ba.

Kara karanta wannan

Masha Allah: Dakarun Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace

Kakakin ya bayar da tabbacin za su ci gaba da yin ƙoƙari wajen ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya tare da bayar da cikakken tsaro a yankunan dake fama da tashin hankali.

Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, dakarun sojojin Najeriya sun fatattaki ƴan binɗiga a wasu ƙauyuka na jihar Zamfara bayan sun yi musayar wuta.

Dakarun sojojin sun kuma halaka huɗu daga cikin ƴan bindigan sannan suka ƙwato miyagin bindigu na babura a wajen ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng