Gwara Gwamnatin Buhari Akan Gwamntin Shugaba Tinubu, Wata Mabaraciya

Gwara Gwamnatin Buhari Akan Gwamntin Shugaba Tinubu, Wata Mabaraciya

  • Wata mabaraciya ta koka kan halin ƙuncin da talaka ya tsinci kansa a ƙasar nan saboda tsadar rayuwar da ake ciki
  • Zainab Ado wacce ke bara a jihar Oyo tace gwara gwamnatin tsohon Shugaba Buhari kan gwamnatin Shugaba Tinubu
  • Mabaraciyar tace a baya suna samun sadaka daga waje mutane amma a yanzu masu bayar da sadakar basu da abinda za su bayar

Ibadan, jihar Oyo - Wata mabaraciya a birnin Ibadan na jihar Oyo, ta bayyana bambancin dake tsakanin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Sadiya Ado wacce ƴar asalin ƙaramar hukumar Wudil ce a jihar Kano, ta bayyana cewa a wajenta gwara gwamnatin Buhari akan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Mabaraciya tace gwara gwamnatin Buhari akan ta Tinubu
Sadiya ta koka kan halin da ake ciki a kasa Hoto: Tribune.com
Asali: UGC

Sadiya ta bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Nigerian Tribune ta yi da ita, inda tace masu basu sadaka a baya yanzu sun daina saboda su ma da kyar su ke samun ɗan abinda za su yi amfani da shi.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Shugaba Tinubu Ya Sake Magana Mai Jan Hankali Kan Matsalar Tsaron Najeriya

Mabaraciyar tace yanzu basu samun sadaka

A kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ba za a haɗa gwamnatin baya ba da ta yanzu. Gwamnatin baya ta fi ta yanzu saboda a lokacin idan mu ka fito bara, mutane suna ba mu sadaka sannan muna samun abinda za mu ci, amma yanzu duk sai a hankali saboda waɗanda su ke bamu basu da shi yanzu. Idan basu da shi, ya za mu yi?"

Bazawarar mai ƴaƴa hudu ta yi bayanin cewa ta zo bara ne daga jihar Kano, saboda ƴan uwan mijinta basu taimake ta ba bayan ya rasu.

"Na zo nan ne saboda halin babu. Mijina ya rasu ya barni da ƴaƴa huɗu sannan ba ni da abinda zan ciyar da su. Hakan ya sanya na zo nan yin bara. Rashin lafiya ya yi na ɗan gajeran lokacin sannan ya rasu shekara biyar da suka wuce, inda ya bar min ƴaƴa huɗu." A cewarta.

Kara karanta wannan

An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

"Tun bayan rasuwar mijina, ƴan uwansa ko ƙwayar hatsin shinkafa basu taɓa kawo min ba domin ni da yaran. Ƴan uwana ne kawai su ka taimaka min daga lokaci zuwa lokaci."

Ta yi muhimmin kira ga gwamnati

Ta bayyana cewa ita da sauran ƴan uwanta mabarata basu jindaɗin halin da suka tsinci kansu a ciki, inda tace za su fi so ace suna jihohinsu da suna da wani abun yi.

Ta roƙi gwamnatin tarayya da ta tsamo talakawa daga cikin talauci saboda sun sha wahala kafin su zaɓe su kan mulki.

Gwamna Ya Ƙare Tallafin N8,000 Na Shugaba Tinubu

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kare shirin Shugaba Tinubu na rabon tallafin N8,000 ga iyalai 12m.

Gwamnan ya bayyana cewa talakawa da dama za su amfana da shiron saboda a wajensu N8,000 kuɗi ne masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng