Za a Fi Shan Wahalar Tashin Dala Fiye da Cire Tallafin Fetur da Aka Yi Inji Masani

Za a Fi Shan Wahalar Tashin Dala Fiye da Cire Tallafin Fetur da Aka Yi Inji Masani

  • Usman Adamu Bello ya yi wa Legit.ng Hausa bayanin tasirin tsarin tattalin arzikin arzikin da aka kawo
  • Masanin yana da digirin BSc, MSc da PhD a ilmin tattalin arziki, yana koyarwa a Jami’ar ABU Zariya
  • Dr. Bello ya yi nazari da rubuce-rubuce a kan abubuwan da su ka shafi tattali da darajar kudin kasa

Kaduna - Usman Adamu Bello masani ne a harkar tattalin arzikin arziki, a fagen ya yi ilminsa na digirin farko zuwa na uku a jami’ar Ahmadu Bello a Zariya.

Legit.ng Hausa ta samu lokaci ta yi magana da Dr. Usman Adamu Bello domin jin ra’ayinsa kan wasu tsare-tsare da manufofin sabuwar gwamnatin Najeriya.

Shugaban Najeriya
Bola Tinubu yana kokarin gyara tattalin arziki Hoto: @Mario9jaa
Asali: Twitter

Menene ra’ayinka game da janye tallafin fetur?

Dr. Usman Bello: Gwamnati ta na ikirarin ba talaka ne yake amfana da tsarin ba, amma gaskiya wannan duk maganar fatar baki ce, ba gaskiya ba ne. Shawarar bankin Duniya ne da sauran manya, kuma an yi garaje wajen cire tallafin. Ko a kasashen da su ka cigaba har su Amurka akwai tallafi a irinsu harkar noma, kiwon lafiya da kudin masu zaman kashe wando.

Kara karanta wannan

An Rasa Inda Tattalin Arziki Ya Dosa, Za a Shafe Kusan Kwanaki 60 Babu Ministoci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tasirin tashin farashin man fetur

Dr. Usman Bello: Musamman a Najeriya tun da akwai arzikin fetur kuma ana tunkaho da shi a Afrika, ya kamata jama’a su samu sauki. Sannan ana fama da mutanen da ke cikin talauci, marasa arziki sun fi masu wadata yawa, amma a halin da ake ciki, an kawo tsarin da ya jawo masu wadatar su na talaucewa. Za a gamu da hauhawan farashin kaya da kuma tsadar rayuwa.

Karya Naira za ta haifar da ‘da mai ido?

Dr. Usman Bello: Wannan shi ne mu ke kira daidaita farashin kudin kasashen waje a ilmin tattalin arziki. Shi ma tamkar cire tallafin man fetur ne da aka yi. Idan kasa ta na shigo da kaya daga kasashen waje, dole ta tsare darajar kudinta.

Illar wannan ya fi na tsarin janye tallafi a mai domin dole ne duk wanda zai shigo da fetur daga kasar waje sai ya nemi kudin ketare. Kuma farashin kudin kasashen waje sun fi yawo fiye da kudin gangar danyen mai a kasuwar Duniya. Bincike ya nuna mana akwai dangantaka mai karfi tsakanin darahar kudin waje da farashin mai. Muddin kudin kasa bai da kyau, fetur zai yi tsada ko da farashinsa bai da tsada a Duniya, idan kuwa kudin kasa yana da daraja, fetur zai kasance da araha ko da ba ta da arzikin danyen mai.

Kara karanta wannan

Tallafin Man Fetur: Taliya, Gari Da Rukunin Abubuwa 5 Da Zaka Iya Saya Da Naira 8,000

Ka na goyon bayan a bude iyakoki domin a samu saukin abinci?

Dr. Usman Bello: A nan sai a duba adadin abincin da mutane su ke bukata a Najeriya, gwamnati ta da alkaluma, idan ba za a iya noma abin da ake bukata ba, sai gwamnati ta ba wasu daidaiku damar shigo da ragowar gibin da ake da shi.

Amma a yanzu ko da za a shigo da abinci daga ketare, zai zo da tsada saboda kudin waje ya tashi, an karya darajar Naira. Maganar da ake yi, CFA 1 ita ce N1.3 a kasuwar canji a yau, ko daga makwabta a Afrika za a kawo kayan abinci, zai yi tsada.

Saboda haka an yi gaggawa wajen aiwatar da tsare-tsaren nan, ya kamata a ce an yi nazari tukuna, an zauna da masana tattalin arziki sun bada shawarar abin da ya dace.

FIRS ta samu N5.5tr

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bukaci Majalisa ta nada Mutanen da Buhari Ya Ki Amincewa da su a Gwamnati

Rahoto ya zo cewa Baitul-mali ya tumbatsa a farkon shekarar nan, shugaban FIRS ya shaida cewa sun tattaro makudan kudin shigan da ba a taba gani ba.

A 2021, Naira Tiriliyan 6.4 aka yi samu, a farkon 2023 har an tara Naira Tiriliyan 5.5. Idan aka tafi a haka, kudin shigan da za a samu zai kai Naira tiriliyan 11.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng