Zargin Daukar Nauyin Ta’addanci: Kotu Ta Hana Lauyoyi Da Yan Jarida Sauraron Shar’ar Tukur Mamu
- Babbar kotun tarayya a Abuja ta ci gaba da sauraron shari'ar Tukur Mamu a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli
- Mai shari'a Inyang Ekwo ya umurci lauyoyi da yan jarida su fita daga harabar kotu yayin sauraron shari'ar Mamu
- Ana dai tuhumarsa da hada baki da yan ta'adda wajen kai harin jirgin kasan Kaduna a bara
Abuja - Channels TV ta rahoto cewa an umurci lauyoyi, masu kara da yan jarida su fice daga harabar wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ake sauraron shari’ar Tukur Mamu.
A lokacin da aka kira karar a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli, lauya daga ofishin Atoni Janar na tarayya, wanda ke gabatar da kara a madadin gwamnatin tarayya, David Kaswe, ya fada wa kotun cewa shaidun su na a kotu domin sauraron shari’ar.
Alkali ya bukaci duk wanda baya cikin karar ya fita daga kotu
Sannan sai Kaswe ya bukaci mai shari'a Inyang Ekwo da ya tursasa umurnin farko da aka bayar a baya, na neman dukkanin bangarorin da basa cikin karar su bar kotun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mai shari'a Ekwo, wanda ya amsa bukatar, ya umurci kowa ya bar kotun, illa bangarorin da ke cikin karar.
Sai dai kuma, ci gaban ya saba wa bukatar masu gabatar da karar na neman a bar yan jarida da aka tantance a babbar kotun tarayyar su sa ido a kan shari'ar.
A ranar Laraba ne Maishari'a Ekwo ya amince da bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar na rufe fuskokin shaidun da aka tara a shari’ar Mamu, wanda ake tuhuma kan alakarsa da yan ta'addar da suka kai harin jirgin kasan Kaduna a shekarar da ta gabata.
Alkalin ya amince da bukatar ne biyo bayan wani kudiri da Kaswe ya gabatar a gaban kotun.
Kotu ta yi fatali da bukatar Tukur Mamu na neman beli
A gefe guda, Legit.ng ta kawo a baya cewa wata babbar kotun tarayya mai zaman ta a birnin tarayya Abuja, ta yi fatali da neman belin da Tukur Mohammed Mamu, ya yi a gaban ta.
A wani hukunci da alƙalin kotun, Inyang Ekwo, ya yanke a ranar Alhamis, ya ce ƙorafin da Mamu ya shigar bai samar da cikakkun hujjojin da kotu za ta yi hukuncin da zai masa daɗi ba.
Asali: Legit.ng