Najeriya Na Daf Da Rasa Kambunta Na 1 Da Ta Fi Karfin Tattalin Arziki A Nahiyar Afirka, An Bayyana Kididdigar

Najeriya Na Daf Da Rasa Kambunta Na 1 Da Ta Fi Karfin Tattalin Arziki A Nahiyar Afirka, An Bayyana Kididdigar

  • Har yanzu Nigeria ce kasar da tafi kowa karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka yayin da Egypt ke biye mata
  • Arzikin Najeriya ya karu da kashi 8.3 a shekarar 2022 da kudin shiga da ya kai $477.4bn
  • Sai dai kasar na fuskantar barazana daga Egypt wacce ta kasance na biyu a jerin kasashe masu arzikin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja – Najeriya ta ci gaba da rike kambun wacce ta fi kowa karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka a 2022 karo na biyar da kudin shiga dala biliyan 477.4.

Najeriya da ta fi ko wacce karfin tattalin arziki ta na dauke da kashi 17.4 na tattalin arzikin Nahiyar da kudin shiga da ya kai dala tiriliyan fiye da 2, Legit.ng ta tattaro.

Najeriya Na Daf Da Rasa Kambun Na 1 Da Ta Fi Karfin Tattalin Arziki A Nahiyar Afirka, An Bayyana Kididdigar
Egypt Na Barazana Ga Najeriya Na Kwace Kambunta 1 Da Ta Fi Karfin Tattalin Arziki A Nahiyar Afirka. Hoto: Kola Sulaimon.
Asali: Getty Images

Sai dai kasar na fuskantar barazanar rasa matsayin daga kasar Egypt da ta sako ta a gaba a matsayi na biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Wata Budurwa Tana Dafa Taliya Da Lemun Mirinda Da Sukari Ya Girgiza Intanet

Najeriya ita ce ta fi kowa karfin tattalin arziki a Nahiyar

Babban Bankin Duniya ta ce Najeriya ta ci gaba da rike matsayin tun shekarar 2018 da ta kwace a hannun Afirka ta Kudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bankin ta ce arzikin Najeriya ya karu da kashi 8.3 a shekarar 2022 daga $440.8bn da aka yi kididdiga a shekarar 2021.

Kasar Egypt ta biyo ta a matsayi na biyu da kudin shiga $476.7 bayan samun karuwa ta fiye da kashi 12.3 a shekarar 2021.

Afirka ta Kudu ita ce a matsayi na uku da kudin shiga da ya kai $405.9bn, inda manyan kasashen da suka fi kowa karfin tattalin arziki suke rike da fiye da rabin arzikin Nahiyar gaba daya.

Sauran kasashen da suka biyo baya sun hada da:

- Algeria: $191.9bn

- Ethiopia: $126.8bn

- Kenya: $113.4bn

- Angola: $106.7bn

Kara karanta wannan

Kowa Zai Samu: Gwamnati Ta Bayyana Yadda Rabon N8000 Na Tinubu Zai Wakana

- Tanzania: $75.7bn

- Ghana: $72.8bn

- Cote d’Ivore: $70bn

Nairametrics ta tattaro cewa kasar Egypt na daf da kamo Najeriya ganin yadda ta samu karuwar tattalin arziki da kashi 12.3 zuwa $476.7bn.

Egypt ta kwace matsayi na biyu a hannun Afirka ta Kudu a shekarar 2022 inda take bin Najeriya ba tare da wata rata a tsakani ba.

Elon Musk Ya Dawo Matsayi Na 1 Da $250bn, Zuckerberg Ya Fado, Dangote Ya Kara Sama

A wani labarin, Alhaji Aliko Dangote ya ci gaba da rike matsayinsa na wanda ya fi kowa arziki a A firka.

Wannan na zuwa ne bayan Dangote ya samu ribar $272 a ranar Juma'a 14 ga watan Yuli.

Mai kamfanin Twitter, Elon Musk ya dawo matsayin wanda ya fi kowa a duniya bayan tafka asarar $200bn a 2022, yayin da mai kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ya tafka asara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.