Tsadar Mai: Gwamnati Za Ta Sauya Amfani Da Fetur Zuwa Gas A Ababan Hawa
- Hukumar Koyar da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT) ta sha alwashin kawo sauki ga ‘yan Najeriya da ke fama da tsadar mai
- Hukumar ta ce za ta sauya motocin mutane da ke amfani da man fetur zuwa Gas ganin yadda Gas din yafi sauki yanzu a kasar
- Shugaban hukumar, Dakta Bayero shi ya bayyana haka ga ‘yan jaridu a hedikwatar hukumar da ke jihar Kaduna
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna – Tun bayan cire tallafin mai a Najeriya ‘yan kasar ke fama da tsadar man fetur da ya ke so ya fi karfin jama’a.
Dalilin haka, Hukumar Koyar da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT) ta yi alkawarin sauyawa jama’a motocinsu zuwa amfani da Gas madadin man fetur.
Shugaban hukumar, Dakta Bayero Salih-Fara shi ya tabbatar da haka ga ‘yan jaridu a hedikwar hukumar da ke jihar Kaduna, Aminiya ta tattaro.
Dakta Bayero ya ce cibiyar ta fara wannan aiki ne tun shekarar da ta gabata inda ya ce suna da ofisoshi a dukkan shiyyoyin kasar nan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya fadi yadda za su sauya motoci daga amfani da fetur zuwa Gas
Ya ce a ko wace shiyya za su koyawa mutane tare da ba su horaswa na musamman don fara gudanar da wannan gagarumin aiki a cikin makwanni masu zuwa, Daily Trust ta tattaro.
Ya kara da cewa a yanzu ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali na tsadar fetur wanda tabbas suna bukatan sauki ta ko wace fuska musamman yadda sufuri ya yi tsada sakamakon haka.
Ya ce yin hakan zai samar da sauki ga jama’a daga amfani da fetur zuwa Gas wanda yafi sauki a halin yanzu, cewar Punch.
Ya roki hadin kan 'yan kasar don samun nasara
Daktan ya roki ‘yan Najeriya da su ba su hadin kai a wannan shiri nasu don ganin an samu nasarar da ake bukata da zai amfani jama’a da samar musu sauki.
A halin yanzu mutane da dama sun sauya injin samar da wutar lantarki mai amfani da man fetur zuwa Gas a fadin Najeriya.
Wannan ya kawo sauki ga mutane da dama wadanda suke yawan siyan man fetur don harkokinsu na yau da kullum.
Arewacin Najeriya Za Ta Samu Gas Da Lantarki, Inji Kamfanin NNPC
A wani labarin, Kamfanin man fetur a Najeriya, NNPCL ya bayyana cewa Arewacin Najeriya za ta samu wadataccen wutar lantarki da gas.
Shugaban kamfanin, Mele Kari shi ya bayyana haka inda ya ce kwangilar AKK da aka dauko daga Ajaokuta zuwa Kano ta kusa kammaluwa.
Yayin kai ziyara zuwa garin Ahoko a jihar Kogi domin ganin yadda abubuwa suke tafiya, Mele Kyari ya tabbatar da cewa an cimma kashi 70 na aikin.
Asali: Legit.ng