Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Borno, Sun Halaka Mutum Shida Da Kwato Makamai Masu Yawa

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Borno, Sun Halaka Mutum Shida Da Kwato Makamai Masu Yawa

  • Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan ta'adda masu yawa a jihar Borno a wani bata kashi da suka yi a cikin kwanaki biyu
  • Dakarun sojojin sun kuma cafke wani tantirin mai yi wa ƴan ta'addan leƙen sirri da haɗi baki da su wajen aikata ta'asa
  • A yayin fafatawar dakarun sojojin sun kwato miyagun makamai, kayan abinci da tsabar kuɗi a hannun ƴan ta'addan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Borno - Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadin Kai' sun salwantar da rayukan ƴan ta'adda shida a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'addan ne a tsakanin ranakun 11 da 12 na watan Yuli tare da cafke mai haɗa baki da ƴan ta'addan, Bulama Suri, rahoton Leadership ya tabbatar.

Sojoji sun halaka 'yan ta'adda a Borno
Dakarun sojojin sun sheke 'yan ta'adda shida Hoto: Thecable.com
Asali: UGC

Darektan watsa labarai na hukumar tsaron ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana haka a lokacin bayar da bayanan ayyukan dakarun sojojin Najeriya a tsakanin ranakun 13 zuwa 20 na watan Yuli, wanda ake yi duk bayan sati ɗaya, a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Ugo: Babban Alkalin Da Ke Jagorantar Shari'ar Neman a Soke Zaben Tinubu Ya Yi Murabus? Gaskiya Ta Bayyana

Manjo Janar Buba, ya bayyana cewa Suri Bulama mai yi wa ƴan ta'adda leƙen asiri ne da haɗa baki da su wanda yake zaune a ƙauyukan Gaulawa da Gwazari na ƙananan hukumomin Kukawa da Konduga, cewar rahoton The Sun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dakarun sojojin sun ƙwato miyagun makamai a hannun ƴan ta'addan

Manjo Janar Buba ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun kwato kayan abinci da shanu biyu a hannun ƴan ta'addan.

Ya bayyana cewa dakarun sojojin a cikin wannan lokacin na sati ɗaya, sun halaka ƴan ta'adda shida da cafke mutum takwas da ake zarginsu da haɗa baki da ƴan ta'addan, yayin da aka ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato miyagun makamai a hannun ƴan ta'addan da suka haɗa da AK47 guda bakwai, bindigu biyu ƙirar FN, gurneti ɗaya, harsasai 100.

Kara karanta wannan

Masha Allah: Dakarun Sojoji Sun Fatattaki 'Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Ceto Mutane Masu Yawa Da Suka Sace

Sauran abubuwan da sojojin suka ƙwato a hannun ƴan ta'addan sun haɗa da wayoyin hannu guda biyu, shanu biyu, kayan abinci, amalanke ɗaya da tsabar kuɗi N2.1m.

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda Ta Sama

A wani labarin kuma, dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' sun yi luguden wuta ta sama kan ƴan bindiga a jihar Katsina.

Dakarun sojojin sun halaka ƴan bindiga 22 a yayin farmakin da suka kai musu a maɓoƴarsu cikin ƙananan hukumomi biyu na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng