Anyi Asarar Dukiya Yayin da Gobara Ta Lakume Shugana a Kasuwar Kano
- Fitacciyar kasuwar nan ta jihar Kano ta kama da wuta a daren ranar Laraba, 19 ga watan Yuli
- Gobarar ta kona shaguna 10 kurmus a kasuwar Rimi da ke garin Kano kamar yadda hukumar kwana-kwana ta tabbatar
- Mai magana da yawun hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce tartsin wutar lantarki ne ya haddasa gobarar inda ya bukaci yan kasuwa da su dunga kashe kayan wuta idan suka tashi kasuwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Jami'an hukumar kwana-kwana sun bayyana a ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli, cewa gobarar cikin dare ta lakume wasu shaguna a kasuwar Rimi da ke jihar Kano.
Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya ce shaguna 10 ne suka kone a gobarar wacce ta afku da misalin karfe 8:40 na daren ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Bidiyon Dala: Kungiya Ta Tada Jijiyar Wuya, Ta Ce Bai Kamata Tinubu Ya Ba Ganduje Da Doguwa Mukamai Ba
Abdullahi ya ce:
"Mun samu wani kira mai cike da damuwa daga wani Magaji Umar cewa an samu tashin gobawa a kasuwar da suke siyar da katifu, gadaje da kayan daki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Da samun labarin, sai muka gaggauta tura wasu jami'anmu da motocin kashe gobara zuwa wajen da misalin karfe 8:49 na dare domin su kashe gobarar don kada ya shafi sauran shaguna."
Shaguna 10 sun kone kurmus a gobarar
Abdullahi ya kara da cewar wasu shagunan dindindin guda shida da shagunan wucin gadi hudu sun kone kurmus yayin da wani daya ya kone kadan.
Ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne sakamakon tartsatsin wutar lantarki daga wani gini da aka gyara, inda ya ce ana kan bincike a kan lamarin.
Kakakin hukumar kwana-kwanan ya ce babu wanda ya jikkata kuma ba a rasa rai ba sannan ya shawarci yan kasuwa da su dunga tabbatar da sun kashe duk kayan wuta da cire su daga jikin bango kafin su bar kasuwar, rahoton Peoples Gazatte.
Cire Tallafi: Muna Dab Da Durkushewa, Dillalan Mai Sun Bayyana Irin Halin Kunci Da Suke Ciki, Sun Nemi Agaji
Gobara ta lalata dukiya a fadar sarkin Daura
A wani labari makamancin wannan, Legit.ng ta kawo a baya cewa an yi asarar kayayyakin miliyoyin naira a gobarar da ta tashi a fadar mai martaba sarkin Daura.
Gobarar wacce ta fara da wajen misalin ƙarfe 4:00 na yammacin ranar Litinin, ta kwashe lokaci mai tsawo tana ci inda ta lalata kusan komai na wani sashi a fadar.
Asali: Legit.ng