Shugaba Tinubu Ya Gana Da Shettima, Akpabio Da Wasu Gwamnoni Kan Rabon Kayan Tallafi

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Shettima, Akpabio Da Wasu Gwamnoni Kan Rabon Kayan Tallafi

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba da daddare ya yi muhimmiyar ganawa da wasu manyan jiga-jigai dangane da halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki
  • Shugaban ƙasar ya gana da Kashim Shettima, Godswill Akpabio da wasu gwamnoni domin kammala tsare-tsare kan yadda za a raba kayan tallafi
  • Haka kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana daga cikin mahalarta taron

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - A ranar Laraba, 19 ga watan Yuli, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu manyan ƙusoshi a ƙasar nan domin kammala tsare-tsaren yadda za a gudanar da rabon kayan tallafi domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Shugaban ƙasar ya gana da mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu gwamnonin jihohin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare Kan Ministocin Shugaba Tinubu, Majalisa Za Ta Karanto Sunayensu a Yau

Shugaba Tinubu ya gana da Kashim Shettima da Akpabio da wasu gwamnoni
Shugaban kasar ya yi ganawar ne domin kammala tsare-tsaren rabon kayan tallafi Hoto: @NTANewsNow
Asali: Twitter

Shugaban ƙasar yana ci gaba da tattaunawa ne da manyan jiga-jigai a ƙasar nan kan yadda za a farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan wanda ya shiga wani hali a dalilin cire tallafin man fetur da aka yi.

Shugaba Tinubu ya gana da Shettima, Akpabio da wasu gwamnoni kan rabon kayan tallafi

A dalilin hakan ne shugaban ƙasa da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima sun gana da shugaban majalisar dattawa da wasu gwamnoni da suka haɗa da na jihohin Imo, Kwara, Legas da Ogun, jaridar Vanguard ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yana daga cikin mahalarta taron.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake ya yi bayanin cewa taron ya yi duba kan yadda za a kammala tsare-tsaren rabon kayan tallafi domin rage radaɗin cire tallafin man fetur, rahoton NTA News ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa da Wasu Gwamnoni 3 a Villa, Bayanai Sun Fito

Tun da farko gwamnatin tarayya ta shirya rabon hatsi da takin zamani ga manoma aɓwanu shiri na ƙara tsaron abinci a ƙasa.

Gwamnati Za Ta Kara Albashin Ma'aikata

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill ya yi bayanin cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta yi wa ma'aikata ƙarin albashi.

Shugaban majalisar dattawan ya yi bayanin cewa za a yi ƙarin albashin ne domin rage raɗaɗin halin ƙuncin da cire tallafin man fetur ya janyo a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng