Cire Tallafi: COEASU Ta Umarci Mambobinta Su Na Zuwa Aiki Kwanaki 2 Kacal A Sati
- Kungiyar Malaman Kwalejin Ilimi (COEASU) ta ba da umarni ga mambobinta da su koma zuwa aiki sau biyu a mako
- Kungiyar ta ce hakan ya zama dole ganin yadda ma'aikatanta suke korafi na zuwa wurin aiki dalilin cire tallafin mai
- Shugaban kungiyar, Dakta Smart Olugbeko shi ya bayyana haka a yau Laraba 19 ga watan Yuli a Abuja
FCT, Abuja - Kungiyar Malaman Kwalejin Ilimi (COEASU) ta umarci dukkan mambobinta su rinka zuwa aiki na kwanaki biyu kacal a sati.
Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Smart Olugbeko shi ya bayyana haka a yau Laraba 19 ga watan Yuli a Abuja.
Ya ce wannan mataki ya biyo bayan ganawar da mambobin kungiyar suka yi ganin halin da ake ciki a kasar bayan cire tallafin man fetur, PM News ta tattaro.
Ya bayyana yadda cire tallafin ya shafi mambobinsu
Olugbeko ya ce bayan Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur a kasar, litar mai ta tashi da kusan kashi 250.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
"Wannan ya kara dakula lamura musamman farashin sufuri da abinci da sauran kayan masarufi da ke shafar talakan kasar.
"Ma'aikata da suka hada da malaman Kwalejin ilimi sun mai da abin ba komai suka ci gaba da rayuwarsu da tunanin cewa wahalar ta dan lokaci kadan ce, tun da gwamnati ta ce za ta bayar da tallafi.
"A karshe, bayan mun gama shan wahala karfin mu ya kare, sai gashi farashin litar mai ta karu zuwa N650.
"Yanzu shugabannin wannar kungiya sun samu korafin cewa mambobinta ba sa iya zuwa aiki saboda halin da ake ciki na tsadar man fetur."
Olugbeko ya ce kungiyar ta umarci mambobinta da su rinka zuwa wurin aiki sau biyu kawai a cikin sati saboda kuncin da suke ciki.
Ya kara da cewa kungiyar za ta sake zama don bayyanawa mambobinta ranakun da ya kamata suna zuwa wurin aiki, The Guardian ta tattaro.
Ya koka kan yadda albashin ma'aikatansu ya ke ba sauyi shekaru 13
Ya kara da cewa:
"Albashin ma'akatan mu an tabbatar da shi ne tun 2010, shekaru 13 da suka wuce.
"Hakan ya nuna cewa muna kan albashi daya tun 2010, yayin da farashin mai ya karu tun daga wannan lokaci daga N65 zuwa N650.
"Albashin da ya kamata ana sauyawa duk bayan shekaru 3 amma yanzu shekaru 13 ba a yi komai ba."
Ya kirayi Shugaba Tinubu da ya yi abinda ya dace akan halin da ake ciki da kuma duba albashin ma'aikatan Kwalejin Ilimi a kasar.
Kungiyar COEASU Ta Jingine Yakin Aikin Ta Na Tsawon Kwana 60
A wani labarin, Kugiyar Malaman Kwalejin Ilimi, COEASU ta ajiye yajin aikin da ta ke yi bayan shafe kwanaki 60.
Kungiyar ta dauki wannan matakin ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na kungiyar da aka yi a Abuja.
COEASU ta fara yajin aikin ne a ranar 10 ga watan Yunin 2022 a wani yunkuri na ganin an biya mata bukatunta.
Asali: Legit.ng