Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Da Ke Gararamba a Gonakin Jama’a Tare Da Musu Barna, Sun Bayyana Matakin Gaba
- Rundunar soji a jihar Plateau ta kama shanu da awaki fiye da 1000 da suke yawo da barna a gonakin jama’a
- Rundunar ta ce ta kama shanun ne a kauyen Dumunan a yankin Bwai da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau
- Kakakin rundunar, Kyaftin James Oya shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Laraba 19 ga watan Yuli a Jos
Jihar Plateau - Rundunar sojin ‘Operation Safe Haven’ ta kama shanu fiye da 1000 da suke ta gantali da shiga gonakin mutane.
Rundunar ta ce ta kama shanun ne a kauyen Dumunan a yankin Bwai da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba 19 ga watan Yuli, kakakin rundunar, Kyaftin James Oya ya ce sun kama awaki da shanun ne don kawo zaman lafiya a yankin.
Rundunar ta bayyana yadda ta kama shanun a gonakin jama'a
Ya ce a binciken da suka gudanar, awaki da shanun sun taso ne tun daga kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi a jihar, PM News ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“A kokarin mu na maido da zaman lafiya a wannan yankin, rundunar mu ta kama shanu da awaki fiye da 1000 da suke yawo a gonakin mutane tare da yi musu barna a kauyen Dumunan.
“Binciken farko ya tabbatar mana da cewa wadannan awaki da shanun sun taho ne tun daga kananan hukumomin Bokkos da Barikin Ladi a jihar.
“Wadannan shanu yanzu haka muna tsare da su don daukar matakin da ya dace.”
Ya ce rundunar ta himmatu wurin dakile rashin tsaro a yankin
Sai dai Oya bai bayyana ko masu shanun suma an kama su ba, ko kuma martani daga masu shanun, Daily Nigerian ta tattaro.
Oya ya bayyana himmatuwar kwamandan ‘Operation Safe Haven’, Manjo Janar Abdusalam Abubakar na ganin ya kawo karshen kashe-kashe da ke faruwa a karamar hukumar Mangu da yankunanta.
Yankunan karamar hukumar Mangu da ke jihar Plateau na fama da hare-haren ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne.
A makwannin da suka gabata an kashe akalla mutane fiye da 200 a kauyuka daban-daban na karamar hukumar, cewar The Guardian.
Sojoji Sun Sheke ’Yan Ta’adda 5 Da Ke Shirin Tsallakowa Najeriya Daga Kamaru
A wani labarin, sojoji sun sheke wasu 'yan ta'adda da ake zargin suna kokarin shigowa Najeriya daga Kamaru.
Sabon daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar ES Buba shi ya bayyana haka a hedikwatar tsaro da ke Abuja.
Ya ce 'yan ta'addan da suka hada da Boko Haram da ISWAP sun gamu da ajalisu ne bayan samun bayanan sirri.
Asali: Legit.ng