"Matana Tana Duka Na Kamar Jaki, Ba Ta Girmama Iyaye Na" Miji Ya Nemi Saki a Kotu

"Matana Tana Duka Na Kamar Jaki, Ba Ta Girmama Iyaye Na" Miji Ya Nemi Saki a Kotu

  • Wani magidanci ɗan ƙasuwa, Raphael Chima ya maka matarsa a gaban Kotun kostumare da ke zama a Abuja
  • Ya yi zargin cewa matarsa ba ta kaunar zaman lafiya, tana dukansa sannan kuma ba ta ganin girman iyayensa
  • Sai dai matar ta ƙaryata bayanin mijinta kuma nan take Alkali ya ba su shawara su koma su sulhunta sabanin da ke tsakaninsu kafin zama na gaba

FCT Abuja - Wani ɗan kasuwa, Raphael Chima, ya kai ƙarar matarsa Misis Joy gaban Kotun kostumare da ke birnin tarayya Abuja bisa zargin rashin son zaman lafiya.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa magidancin ya zargi matarsa da masifa ako wane lokaci a cikin ƙarar da ya shigar da matar a gaban Kotun ranar Talata, 18 ga watan Yuli.

Rikicin ma'aurata a Kotu.
"Matana Tana Duka Na Kamar Jaki, Ba Ta Girmama Iyaye Na" Miji Ya Nemi Saki a Kotu Hoto: thenationonline
Asali: Twitter

A jawabinsa, Mista Chima ya ce:

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Magantu Kan Batun Ciyo Bashin Biliyan 10 Don CCTV, Ya Fayyace Gaskiyar Al'amari

"Gaba da gaba matata take zagi na kuma ta ci mutunci na ba bu kunya. Ko ɗan ya ta samu dama ta kan zabga mun mari, tana zagi na da cewa ni mahaukaci ne."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma ɗan kasuwan ya ƙara da faɗa wa Kotu cewa matarsa ba ta ganin girman iyayensa duk da kasancewarsu sirikanta.

Bayan haka, mai shigar da ƙarar ya yi bayanin cewa matar ta bar masa yaron da Allah ya ba su a zaman auren, shi kaɗai ke kokarin kulawa da ɗansu ba tare da taimakonta ba

Bisa haka ya roƙi Kotun ta ba shi damar ci gaba da rainon yaron kana ta datse igiyoyin aurensa da matar, kowa ya kama gabansa.

Shin matar da amince da tuhumar da mijinta ke mata?

Nan take wacce ake ƙara kuma matar ɗan kasuwan, Misis Joy ta musanta dukkan zargin da abokin rayuwarta ya ɗora mata a gaban Kotu.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Masoyin Tinubu Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, Ya Yi Iƙirarin Daukar Mummunan Mataki

Alkalin Kotun mai shari'a Dada Oluwaseyi ya shawarci ma'auratan su koma gida su duba yuwuwar sulhunta saɓanin da ke tsakaninsu don samun zaman lafiya.

Daga nan Alkalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga watan Yuli, inda zai saurari sulhun da suka yi a tsakaninsu, NAN ta rahoto.

“Soyayya Ta Gaskiya”: Bidiyon Yadda Aka Tuka Amarya da Ango Zuwa Wajen Biki a Baro Ya Dauka Hankali

A wani rahoton na daban Wani bidiyo da ya yadu ya nuno lokacin da aka tuka wani ango da amaryarsa zuwa wajen bikinsu a cikin baro.

Angon da amaryarsa sun hau kan baron sannan wasu matasa suka taru suka tuka su har zuwa wajen daurin aurensu, lamarin da ya ja hankalin jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262