“Ni Ba Barawo Ba Ne, Na Tafi Da Ita Ne Kawai Ba Da Izini Ba”: Wanda Ake Zargi Da Satar Motar N55m Ya Yi Bayani
- Wani matashi da ya tsere da motar naira miliyan 55 ya bayyana cewa ba da nufin satay a tafi da motar ba
- Matashin wanda ake wa lakabi da ‘Big Shark’ ya bayyana cewa ya tuka motar ne kawai daga Abuja zuwa Delta ba da izinin mai ita ba
- Ya kuma bayyana yadda ya shafe sama da sa’o’i uku yana jiran mai motar a lokacin da ya tafi ciro kudi a wani wajen cirar kudade
Abuja - Matashin da ake zargi da satar mota, Meshach Isinugo wanda aka fi sani da Big Shark, ya musanta zargin satar wata mota kirar Mercedes Benz daga wurin wani mai sayar da motoci.
Matashin ya bayyana cewa ya tuka motar ne kawai daga Abuja zuwa jihar Delta ba tare da sani mai ita ba.
Jaridar The Punch ta ruwaito wani mai sana’ar sayar da mota, Mohammed Manga, wanda ya ce wani mai suna Henry ya tsere da wata motarsa kirar Mercedes Benz GLB 250 wacce kudinta ya haura N55m a yayin da ya je gwaji.
Yadda Big Shark ya arce da motar sama da miliyan 55
Big Shark ya bayyana cewa ya yanke shawarar ya dan yi amfani da motar ne faka-faka a sanda mai motar ya fita domin ya ciro kudi a wani gidan mai, yayin da suka je gwaji kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamishinan ‘yan sanda Wale Abass yayin da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa wani mai sana’ar motoci ya kawo musu rahoton cewa wani mai suna Big Shark, ya gudu da motarsa Mercedes Benz kirar 2021, a ranar 30 ga watan Yuni.
Abass ya kara da cewa jami’ansu sun je garin Ughelli da ke jihar Delta, inda a nan ne suka yi nasarar gano motar da aka bari a cikin jeji.
Wanda ake zargin a yayin da yake amsa tambayoyi daga jami’an hukumar ‘yan sanda, ya bayyana cewa sunan da ake kiransa da shi wato ‘Big Shark’, ya samo asali ne tun a lokacin yarintarsa.
Ni ba barawo ba ne, amma motar dai ba ta wa ba ce – Big Shark ya yi bayani
Big Shark ya ce shi dan asalin garin Ugheli da ke jihar Delta ne, amma a yanzu haka yana zaune ne a Abuja inda yake sana’ar canjin kudaden kasar waje.
Ya kuma ce kasuwancin na sa ya kan kai shi har zuwa kasashen ketare irin su Instanbul da ke kasar Turkiya.
Ya bayyana cewa an kama shi ne a ranar 6 ga watan Yuli, bayan diddikinsa da ‘yan sanda suka bi a yayin da a cewarsa “ya matsar da wata mota daga Abuja zuwa jihar Delta.”
Wani bangare na kalamansa na cewa:
“Ban saci motar ba, amma ba tawa ba ce. Abin da ya faru shi ne, na sami lambar mai motar a wani dandalin yanar gizo.”
“Ya dora hoton motar yana neman mai saye. Lokacin da na kira shi sai ya ce in zo a duba motar in gani. Shi ma mazaunin Abuja ne kuma wurin da ya kira ni a yankin Garki yake.”
Ya kara da cewa da suka fara ciniki ne sai mai motar ya ce masa su tafi gwaji domin ya san abin da zai saya.
Big Shark ya yi kokarin tuntubar mai sayar da motocin
Big Shark ya kuma kara da cewa a yayin gwajin ne mai motar ya nemi da ya jira shi ya ciro kudi ya dawo.
Sai dai ya ce ya jira shin a sama da sa’o’i uku ba tare da ya dawo ba, wayarsa kuma ba ta shiga ba a lokutan da ya kira shi.
Bayan motar ta kwana a hannunsa ne washegari ya tafi jihar Delta da ita domin harkokinsa na kasuwanci.
Big Shark ya ce sai ganin hotunansa ya yi a yanar gizo kan cewa jami’an tsaro na nemansa bisa zargin satar mota.
Ya bayyana cewa shi ba satar motar ya yi, illa iyaka ya tuka ta ne daga Abuja zuwa jihar Delta ba tare da izini ba.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an mayar da wanda ake zargin zuwa Abuja inda ya aikata laifin domin ci gaba da bincike.
Barayi sun tafkawa Fafaroma Benedict mummunar sata
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoton yadda wasu barayi da ba a iya gane ko su waye ba suka tafkawa shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika gagarumar sata.
Barayin sun sace kuros din Fafaroman tare da yin awon gaba da wasu kudade masu yawa.
Asali: Legit.ng